HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 22.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

Aci,gaba da arangama dake faruwa a tsakanin dakarun sojin Amurka da yan fadan sari ka noken garin Falluja,a yauma juma a dakarun mamayen karkashin jagorancin Amurka sun gudanar da hare haren bama bamai da kana nan jiragen yaki a garin na Falluja.

Hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan fadan sari ka noken bakwai wasu kuma da dama sun jikkata. Jamian sojin na Amurka sun shaidar da cewa suna kai wadan nan hare haren ne izuwa maboyar magoya bayan Abu Musab Al Zarqawi da akace suna da mafaka a garin na falluja.

Wan nan dai hari yazo ne a dai dai lokacin da dakarun sojin Biritaniya 650 ke shirin iasa birnin Bagadaza don taimakawa wajen murkushe aiyukan yan fadan sari ka noke dana kwanton baunar dake birnin da kuma wasu garuruwa dake kusa da bagadazan.

A wata sabuwa kuma bayanai sun shaidar da mutuwar wasu yara mata kana na su biyu,sakamakon fado musu da wata roka tayi da sojojin Amurka suka harba izuwa wasu yankuna da yan fadan sari ka noke ke boye a garin Falluja.

Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daya fito daga bakin dakarun sojin na Amurka dangane da faruwar wan nan al,amari,to amma jamian asibitin garin na Falluja sun tabbatar da mutuwar wadan nan yara guda biyu.

A daya hannun kuma wani bom ya fashe a cikin wata karamar mota kusa da ofishin yan sanda dake birnin Bagaza,wanda hakan yayi sanadiyyar jiwa wasu yan sandan biyu rauni.

Yan sandan dai sun shaidar da cewa anyi niyyar tashin bom din ne ga wata twaga ta sojin Amurka dake wucewa a hanyar,to amma hakan bai samu faruwa ba sai da tawagar ta wuce tukuna kana bom din ya tashi.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kusan ko wace ranar Allah ta ,ala sai dakarun Sojin na Amurka sun gudanar da hare haren bama bamai a garin na Falluja bisa zargin cewa Abu musab Al zarqawi na boye a garin tare da jamian sa.

Kungiyyar Abu musab Al zarqawi dai tuni take yin ikirarin cewa tana da hannu a cikin hare haren da ake kaiwa dakarun sojin mamayen a iraqi,wanda bisa hakan ne sojojin suka tashi tsaye wajen neman sa ruwa a jallo.

Don tabbatar da ganin cewa an samu nasar cafke Abu Musab Al zarqawin tuni kasar Amurka tasa tukwicin dalar Amurka miliyan 25 ga duk wanda yayi sanadiyyar kama shi ko kuma ya kama shi da hannun sa.

Har ila yau a waje daya ,kuma rahotanni da suka iso mana daga garin Baquba sun shaidar da cewa anyi wata arangama a tsakanin dakarun sojin na Amurka da wasu yan fadan kwanton bauna,wanda hakan ya haifar da jiwa wasu mutane fararewn hula guda hudu muggan raunuka.

A daya hannun kuma bayanai sun shaidar da cewa anyi musayar wuta mai tananin gaske a tsakanin sojin na Amurka da kuma wasu mabiya addinin musulunci a garin Mosul.

Ya zuwa yanzu dai babu wani labari na rasa rayuka ko kuma fuskantar jikkata daga wadan nan bangarori guda biyu.

Ibrahim Sani.