HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 25.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

Dakarun sojin Amurka a garin Mosul

default

Bayanai da suka iso mana daga kasar ta iraqi sun shaidar da cewa ya zuwa yanzu kungiyyar nan ta Alqeeda da Abu Musab Al zarqawi kewa jagoranci tuni tayi ikirarin cewa tana da hannu dumu dumu a ckkin kisan gillar jamian tsaron kasar ta iraqi su guda 49.

Wan nan ikirari dai na kungiyyar ta Abu Musab Alk zarqawi an same tane a cikin fasahar yanar gizo gizo,wato internat a turannce.

Idan dai za a iya tunawa a farkon makon nan da muke ciki ne yan kungiyyar ta Abu Musab Al zarqawi sukayiwa jamian tsaron na iraqi kwanton bauna a wata cibiyar bincike dake kusa da inda suka karbi horo na musanman.

A cewar rahotannin da suka iso mana magoya bayan Abu Musab Al zarqawin sun harbe jamian tsaron na iraqi ne daya bayan daya bayan duk sun umarce su dasu kwanta a kasa a can iyakar kasar iraqi da iran.

Wan nan al,amari dai ya faru ne a cewar bayanan da suka iso mana jim kadan bayan jamian tsaron sun kammala karbar horo na musanman don fara aikin tabbatar da doka da kuma oda a cikin kasar ta iraqi.

Gamsassun bayanai dai sun shaidar da cewa kungiyyar ta Amu Musab Al zarqawi ta gudanar da wan nan danyan aikin ne bisa hujjar cewa jamian tsaron zasu gudanar da aikin tsaron ne karkashin jagorancin dakarun kasar Amurka,a kuma karkashin gwamnatin da suke ganin ba halastacciya bace.

A yayin da ake cikin wan nan jimami a sai gashi a yau litinin kuma wani bom ya tashi a kusa da ofisoshin dakarun mamaye dake birnin Bagadaza.

Faruwar wan nan al,amari dai yayi sanadiyyar mutuwar yan iraqi biyu wasu kuma guda uku sun jikkata.

Har ila yau rahotannin sun shaidar da tashin wani bom din a can yammacin birin na Bagadaza,wanda hakan yayi sular mutuwar sojan Amurka daya wasu kuma guda biyar suka samu raunuka.

A daya hannun kuma wasu gamsassun bayanan daga iraqi sun tabbatar da tashin wani bom a cikin wata karamar mota a can garin mosul,wanda hakan yayi ajalin daya daga cikin shugabannin kabilar yankin,a hannu daya kuma ya jikkata wasu na hannun daman sa guda biyu.

A cewar wasu jamiai na garin wan nan bom din an dasa shine a cikin motar Sahir Khobar,to amma bai tashi ba tukuna sai da motar ta tsaya a cikin wani gareji a garin na mosul dake yamma da birnin Bagadaza.

A karon farko kuma tun kammala yakin kasar ta iraqi a yau an kaiwa sojin Australia hari na wani bom,wanda hakan yayi yayi ajalin wasu yan kasar ta iraqi guda uku,kana a daya hannun yajiwa wasu sojin kasar ta Austaralia uku rauni iri daban daban.

A wata sabuwa kuma shjugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato Mohd El baradei yace hukumar sa ta rasa gano inda aka tara wasu makamai masu fashewa da aka kwace daga hannun tsohuwar gwamnatin Saddam Hussain.

A cewar Mohd El Baradei wadan nan abubuwa babu su babu alamar su,wato a takaice dai an nemi su an rasa.

El baradei bai tsaya a nan ba domin kuwa ya shaidar da cewa gurin da aka ajiye wadan nan abubuwa,akwai rahoton cewa wasu batagarin yan kasar na ghudanar da halin bera a ciki.

A karshe shugaban hukumar ta IAEA yayi fatan kada wadan nan makamai su fada hannun yan taadda ko kuma masu gabatar da aikin taaddanci a kasar ta iraqi ko kuma wata kasa ta duniya.

Ibrahim Sani.