HALIN DA AKE CIKI A IRAQI | Siyasa | DW | 15.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI

sojojin amurka a falluja

default

Har yanzu dai bata sake zani ba game da arangama dake faruwa a tsakanin dakarun Amurka dana fadan kwanton bauna a garin Falluja na kasar iraqi. Bayanai da suka iso mana sun shaidar da cewa kana nan jiragen yakin na Amurka naci gaba da ruwan bama bamai a wasu yankuna da suke zaton yan fadan kwanton baunar na boye a ciki.

A daya hannun kuma wasu dakarun na amurka naci gaba da laluben inda yan fadan kwanton baunar suke.

wadan nan dai dakarun sojin na gudanar da wan nan laluben ne lungu lungu da kuma sako sako a garin na falluja don neman inda ya kwanton baunar suke.

A cewar kwamandan sojin Amurka dake jan ragamar kai farmakin a garin na Falluja ya shnaidar da cewa bayan tsawon kwanaki bakwai ana fafatawa a yanzu haka sojin sune ke rike da yawa daga cikin yankunan garin na Falluja ciki kuwa har da yankin da yan fadan sari ka noken ake zato suke.

Bugu da kari kwamandan ya kuma tabbatar da cewa dakarun su sun rasa mutane a kalla 38 wasu kuma da yawa sun jikkara a tsawon wan nan mako guda da akayi ana bata kashi a tsakanin su da yan fadan kwanton baunar.

Bayanai dai sun nunar da cewa koda a yau litinin sai da dakarun sojin na Amurka suka kara wani ruwan bama baman a garin na Falluja. Daukar wan nan mataki dai a cewar bayanan da suka iso mana nada alaka nwe da kokarin da suke na tabbatar da doka da kuma oda a fadin garin na Falluja baki daya.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labaru na Reuters daya zaga cikin garin na Falluja a safiyar yau litinin ya rawaito cewa yaga ruguzau na gine ginen kwana da masallatai da coci coci barkatai san nan a hannu daya kuma wayoyin wutar lantarki dana tarho duk sun karkatse abin dai sai wanda ya gani.

A wata sabuwa kuma ofishin tsaro na Amurka ya shaidar da cewa a kalla yan fadan sari ka noke Dubu daya ne suka rasa rayukan nasu kana a daya wajen kuma aka cafke daruruwan su a cikin wadan nan kwanaki bakwai.

Babban dai abu da yanzu haka yafi daukar hankalin mutane a kasar ta iraqi shine yadda zaayi a dawo da mutane dubu 150 da sukayi kaura izuwa wasu garuruwan don tsira da rayukan su daga garin na Falluja a tsawon wadan nan kwanaki bakwai.

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ya zuwa yanzu tuni kungiyyar su ta aike da abinci cike da manya manyan motoci guda bakwai izuwa garin na Falluja don taimakawa wadanda wan nan hargitsi ya rutsa dasu.

Game da kuwa da tantana da ake na ire iren mutanen da suka rasa rayukan nasu a garin na Falluja, Faraministan kasar Iyad Alawi ya shaidar da cewa yayi amanna da cewa dukkanin mutanen dfa suka rasa rayukan nasu a garin na Falluja yan fadan kwanton bauna ne ba wai mutane ne fararen hula ba kamar yadda wasu suke zato a can baya.

Gidan talabijin na Al jazera ya rawaito wani jamii na hukumar bayar da agajin gaggawa na kasar ta iraqi na fadin cewa mutane fararen hula da basu ji basu gani ba sun rasa rayukan nasu da dama a sakam,akon afkawa garin na Falluja da yaki da dakarun Amurka sukayi na tsawon kwanaki bakwan.

Daga can kuma garin Baquba bayanai sun shaidar da cewa da safiyar yau litinin anyi wata mummunan arangama a tsakanin dakarun Sojin na Amurka da kuma y