HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 10.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

jamian tsaro a iraqi na bada hannu akan titi.

default

Rahotanni a yanzu haka da suka iso mana daga kasar ta Iraqi sun nunar da cewa makonni kusan uku a gudanar da zaben gaba gari a kasar, a dai dai lokacin ne kuma harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a fadin kasar baki daya.

Bayanai dai daga kasar sun shaidar da cewa a tsawon mako guda daya gabata an kiyasta cewa mutane sama da dari ne suka rugamu gidan gaskiya sakamakon rikice rikice da tashe tashen hankula iri daban daban a fadin kasar baki daya.

A yayin da kuwa ake cikin wan nan hali a dai dai lokacin ne kuma mabiya darikar sunni ke nuna alamun kin shiga wan nan zabe na gama gari da aka shirya gudanarwa a karshen wan nan wata da muke ciki.

Bayanai dai daga kasar sun shaidar da cewa yan darikar ta sunni na muradin ganin dakarun Amurka a kalla dubu dari da hamsin sun fice ne daga kasar kafin a gudanar da wan nan zabe. Bisa hujjar cewa babu yanda zaayi a gudanar da zabe bisa adalci da gaskiya idan dakarun Sojin na Amurka na cikin kasar ta iraqi.

Ya zuwa yanzu dai mabiya darikar ta Sunni sun nuna bukatar su ta gudanar da taron koli na musanman da dakarun sojin na Amurka don tattauna wan nan bukata tasu.

To amma a ya zuwa yanzu wata majiya daga dakarun sojin na Amurka na nuni da cewa yan darikar ta sunni sun gabatar da wan nan bukatar tasu ne a gajeren lokaci a don haka da alama wan nan buri nasu ba zai samu biyan bukata ba.

A daya hannun kuma ba wai kawai yan darikar sunni ne ke son a dage wan nan zabe na shugaban kasa ba har ma da ragowar mabiya darikun kasar. Hakan kuwa a nasu dalilin ya biyo bayan rashin tabbataccen tsaro ne da babu shi a fadin kasar baki daya.

Wanda bisa hakan ne suke kokari tare da muradin ganin an dage lokacin wan nan zabe ya zuwa wani lokaci a nan gaba kadan.

A dai karshen makon daya gabata, faraministan kasar ta Iraqi Wato Iyad Alawi ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa naci gaba da shirye shiryen gudanar da wan nan zabe duk kuwa da rashin halin tsaro da ake ciki yanzu haka.

Don ganin wan nan aniya tasu ta samu wanzuwa yadda suke so, a yanzu haka rahotanni sun shaidar da cewa tuni gwamnatin ta Alawi tayi nisa wajen gayyato manya manyan shugabannin darikar ta sunni a kasar ta iraqi don tattauna matakan sulhu,bisa hujjar aiwatar da zaben kamar yadda aka tsara shi a tun da farkon fari.

Ya zuwa yanzu dai babban abin da yafi daukar hankali a kasar ta iraqi,musanmamma a tsakanin kabilun kasar shine na tattauna hanyoyin yadda za a dage ranar gudanar da wan nan zabe bisa hujjar farko das suka bayyana. To amma a daya hannun gwamnatin kasar da kuma mahukuntan Amurka sun ke kasa kasa na cewa sai an gudanar da wan nan zabe yadda aka tsara shi tun da farko.

A waje daya kuma kakakin sojin na Amurka a iraqi wato Bob Callahan cewa yayi babu rana ko kuma wata na ficewar dakarun sojin na Amurka dagas kasar ta iraqi. Ficewar su daga kasar inji kakakin ya dangana ne kawai da irin ci gaban da aka samu na tsaro a fadin kasar baki daya.

Ibrahim sani.