Halin da ake ciki a Iraqi | Labarai | DW | 11.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Iraqi

Akalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu yau a kasar Iraki,wanda suka hadar wasu 14 acikin wata karamar Bus din pasinja ,dake dauke da tawagar kuratan soji matasa daga suka fito daga cibiyar horaswa.Wadannan kuratan sojin dai sun gamu da ajalinsu ne,ayayinda wani dan kunar bakin waken dake tafiya cikin wata mota yayi taho mu gama da motar da suke tafiya cikinta,bayan kammala horonsu na yau.A garin Beni saad dake arewacin bagadazan kuwa ,an kaiwa masallacin yan shiaa har,inda aka kashe mutane 7 nan take.Kazalika wasui yan bindiga dadi a garin Diyala,sun harbe wani jamiin soja tare da raunana dansanda,ayayinda tashin wani bomb da aka dasa a gefen hanya ya kashe wani mutum dake tafiya da dansa.

Hakanan kuma a babbar kasuwar garin Baquba wasu yan bindiga dadi sun harbe wani dan Irakin tare da raunana wasu,a harin da suka kai a tashar bus bus dake wannan kasuwa:

 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5T
 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5T