1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraqi

Hauwa Abubakar AjejeOctober 23, 2006

Kasar Amurka na ci gaba da hasarar sojojinta a Iraqi,yayinda a daya hannun ake ci gaba da kira ga Bush da Tony Blair dasu sake duba dabarunsu game da Iraqin.

https://p.dw.com/p/Btxe
Bush da Blair
Bush da BlairHoto: AP

Ci gaba da samun labaru marasa dadi daga Iraqin, fiye da shekaru 3 da rabi bayan dakarun Amurka sun mamaye kasar,tare da kuma da hambarar da gwamnatin Saddam Hussein,ya sanya Karin matsin lamba akan musamman shugaba Bush daya canza dabarunsa akan Iraqin.

Makonni 2 yanzu kafin zaben yan majalisa a Amurka,abokan hamaiyar Bush da ma membobin jamiyarsa ta Republican suna bukatar ganin sabbin dabaru da zasu kawo nasarar yaki a Iraqin ko kuma dawowa da sojin Amurka 142,000 gida.

A dai ranar asabar ne Bush ya gana da manyan janar janar da jamian diplomasiya na yankin gabas ta tsakiya,amma bai sanarda wasu sabbin shawarawari baduk da rahotanni da kafofin yada labari suka bayar na cewa,zai yi kara matsa lambar gwamnatin firaminista Nuri al_Maliki ta kwance damarar yakin kungiyoyi masu makamai.

Yakin nemo kwato Bagadaza ya sake halaka wasu sojojin Amurkan 5,yayinda ake bukukuwan sallah a kasar ta Iraqi tare da kisan wasu yan sanda 17.

Yanzu haka dai cikin wannan wata kadai Amurka tayi hasarar sojojinta 85,wata mafi muni ga sojin na Amurka tun 2005,lokacinda sojin na Amurka suka fafata da yan tawaye a Fallujah.

Tun daga wancan lokaci kuwa sojin Amurka suke fuskantar barazana ga aiyukansu a cikin kasar ta Iraqi da suka mamaye.

Inda aka aike da sojin Amurka 15,000 zuwa birnin Bagadaza,cikinsu har da bataliyan ta Alaska da aka suke da horo mafi inganci na dabarun yaki,amma har yanzu bata canza zani ba.

Yanzu haka dai mataimakin firaministan Iraq Barham Saleh wanda ke birnin London don ganawa da Tony Blair yayi gargadin cewa bai kamata Amurka da Burtania su bar tsoro ya shiga harkokin sake shirya wasu dabaru na shawo kan matsalar Iraqi ba,yana mai kira garesu dasu kara baiwa gwamnatinsa dama game da tsaron kasar.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa,Tony Blair zai kara matsawa mataimakin firaministan na Iraqi lamba game da shirin jamian tsaron kasar na karbar harkokin tsaro daga hannun dakarun Burtaniya a kudancin Iraqi nan da shekara guda.

Sai dai ofishin Tony Blair ya karyata cewa zasu tattauna batun janyewar sojin Burtaniya daga yankin.

Blair dai ya lashi takobin ci gaba da bin manufofinsa na janyewa sannu a hankali,yayinda jamian tsaron Iraqin suka shirya kula da tsaron kasar.

Cikin wani hari daya kara baiyana irin matsalar da Washington da London suke ciki wajen dauka tare da horasda jamian tsaro na Iraqi,a jiya lahadi kadai yan sanda 13 sun halaka wasu kuma 25 suka jikkata cikin wani harin kwantan bauna kan motocinsu da akayi a Baquba.

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka James Baker yanzu haka yana shugabantar wani komiti dake shirya sabbin dabaru a Iraqi,wanda wasu ke ganin cewa cewa mai yiwuwa gwamnatin Bush ta fake da shawarar komitin wajen janyewa cikin wayo daga Iraqin.

Tsohon jakadan Burtaniya a majalisar dinkin duniya Sir Jeremy Greenstock ya sanarda gidan TV na Sky cewa, yanzu haka dabaru da suka saurawa sojin kawance sai hanyoyi marasa kyau.