HALIN DA AKE CIKI A IRAQI A YAU | Siyasa | DW | 30.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI A YAU

A yau juma,a wasu yan kwanton bauna a arewacin kasar Iraqi sun budewa wasu jamian tsaron sa kai wuta a cibiyar da suke gudanar da cakin cakin na abubuwan hawa a can kusa da garin Kirkuk. Musayar wutan a tsakanin jamian tsaron sa kann da yan fadan sari ka noken ya haifar an kashe daya daga cikin yan kwanton baunan kana a daya hannun kuma an jiwa daya rauni. A cewar daya daga cikin jamian tsaron yan sanda na kasar mai suna Shirku shakar,yan fadan kwanton baunar sun budewa jaman tsaron wuta ne jim kadan bayan isowar su izuwa gurin da suke gudanar da aikin tsaron dake arewa da garin kirkuk,wanda yayi dai dai da misalin kilomita 250 daga birnin Bagadaza. Brigadiya shikru yaci gaba da cewa ganin hakan ne ya haifar jamian tsaron suka mayar da martani ta hanyar bude wuta kann abokan gabar ba tare da wani bata lokaci ba. Wan nan dai hari kann cibiyar tsaron ta kusa da garin kirkuk a cewar Shikru ya kasance hari na biyu a tsawon kwana biyu da suka gabata,wanda yan fadan sari ka noken ke kai hare hare na kwanton bauna. Bugu da kari Shakar ya kuma tabbatar da cewa sojojin Amurka a yau juma,ar sun taimaka wajen kawar da wani bom dake cikin wata mota,wanda yan fadan sari ka noken suka sa a kann hanyoyin da motocin daukar mai da kuma tankunan yaki na Amurka kebi. Jami,in yan sandan ya kara da cewa sojojin kasar Japan ne suka gano motar a yashe a kann titin wanda hakan ya haifar suka gudanar da bincike na gaggauwa a kanta,a karshe kuma suka gano cewa makirci ne aka hada a cikin motar don kawo hari ga motocin sojojin taron dangin dake cikin kasar ta Iraqi. A yanzu haka dai rahotanni a kasar ta iraqi sun nunar da cewa ire iren hare haren kunar bakin wake da ake kaiwa a cikin kasar ana yinsa ne kann yan kasar ta iraqi dake taimakawa sojojin Amurka gudanar da aikin su a cikin kasar. Rahotannin sun shaidar da cewa koda a jiya alhamis sai da wasu jamian tsaron sa kai su 11 suka jikkata a sabili da tashin wani bom a can garin Baqouba. Haka kuma a can garin Ramadi,wanda da dama daga cikin mutanen garin yan goyon bayan tsohon shugaban kasar ne wato saddam Hussain sun shaidar da cewa sun sami takardu dauke da rubuton kashedi na daina yiwa sojojin taron dangin aiki nan da kwanaki 10 masu zuwa ko kuma mutun ya dandana kunar sa. A kuwa ta bakin shugaban rundunar sojin Amurka dake kasar ta iraqi, Ricado Sanchez, bisa ire iren abubuwan da suke faruwa a kasar da alama kungiyyar Alqaeeda ta fara samun gindin zama a cikin kasar ta iraqi,wanda ya zama dole sojojin mu su kara kaimi don dakile aiyukan ire iren mutanen dake da nasaba da kungiyyar ta Qlqaeeda. Sojojin kasar ta Amurka a tun can baya sun sha zargin magoya bayan Saddam hussain da kuma mambobin jamiyyar sa ta Bath Party da shirya manakisar hare haren kwanton bauna dana sari ka noke da ake kai musu a kai a kai a fadin kasar ta iraqi baki daya.