HALIN DA AKE CIKI A IRAKI | Siyasa | DW | 29.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAKI

Thailand da Bulgaria sun lashi takobin cewa dakarunsu zasu cigaba da kasancewa a Iraki,duk da barazanar hare hare da suke fuskanta.Itama kasar japan ta mika sunanta cikin jerin sunayen da Amurka take nema su yafewa Iraki basussuka da suke binta.

To sai dai a wani dauki ba dadi daya gudana tsakanin dakarun Amurka da yan yakin sunkuru a birnin Mosul dake arewacin Iraki,sun fidda wata sanar dake nuni dacewa sun bindige mayakan uku,kana sun cafke yan Orakin guda shida harda kananan yara 3.Dakarun na Amurka dai sunyi amfani da makamaui masu linzami wajen lalata wannan gida.

A ranar asabar ne kuma akayi wasu hare haren boma bomai,Rokoki tare da kunar bakin wake daya kashe mutane 19,5 yan Bungaria,biyu sojojin Thailanda da yan Iraki 12 a garin Karbala.Washe garin wadannan hare hare ne boma bomai na gefen titi ya ritsa da rayukan sojojin Amurka biyu,daya a cikin Bagadaza ayayinda gudan kuwa a garin Falluja.

Harin na Bagadaza ya kuma ritsa da rayukan yan Iraki guda biyu,ayayinda sojojin Amurka 5 suka samu raunuka.wannan ya kawo ga adadin dakarun Amurka 327 kenan sukq bakunci lahira ta wannan hanya,tunda Amurka ta jagoranci kawayenta wajen Afkawa Iraki a watan Maris din wannan shekara da muke ciki. To hannu guda kuma Tsohon shugaba Sadam Hussein ya bayyanawa masu bincikensa inda wasu makamai ke boye,da kuma kudi kimanin dala billion 40,wanda ya mallaka alokacin daya ke karagar mulkin Iraki.Bugu da kari ya sanar da sunayen wadanda suka taimaka wajen yi masa ajiyan wadannan makuddan kudade a susun kasashen ketare.Daya daga cikin yan majalisar zartarwa na Iraki Iyad Allawi ya bayyana cewa,a halin yanzu an fara binciken wadannan kudaden da aka ce anyi ajiyansu a asusun bankuna a kasashen Switzerland,Jamus,Japan da wasu kasashe akarkashin sunayen kamfanoni na karya.To sai dai Allawi yace abunda har yanzu baa gano ba shine ko Sadam yana da hulda da kungiyoyin yan taadda.Bugu da aa tantance dangantakar Sadam da hare haren yan yakin sunkurin dake cigaba da gudana a Iraki ba duk dacewa tsohon shugaban na hannu,musamman dauki dai dai da ake yiwa sojojin Amurka tunda Shugaba Bush ya sanar da mamaye a ranar 1 ga watan mayun wannan shekara da muke ciki.Amurkan dai na zargin yan yakin sunkurun da kasancewa magoya bayan Sadam.

 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmu
 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmu