HALIN DA AKE CIKI A IRAKI | Siyasa | DW | 26.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAKI

Dakarun Amurka tare da agajin yan Iraki na cigaba da binciken gaban bakin kogin Tigris dake arewacin Iraki,a dangane da sojin Amurka guda da matuka jirgi 2 da suka bace bayan faduwan jirginsu kirar saukan Ungulu,alokacinda suke neman wani jirgin ruwa na sintiri daya nitse a kogin.A wannan hadarin dai yansandan Iraki biyu tare da mai fassara guda,dake tare da Amurkawan sun rigamu gidan gaskiya,ayayinda har yanzu baa san inda daya daga cikin sojojin yake ba,kana uku sun tsira da rayukansu. A ranar lahadi da yammaci ne jirgin yakin na Amurka ya fadi a garin Tigris dake arewacin birnin Mosul,ayayinda da suke aikin bincike da kuma agaji wa wadanda hadarin nitsewan jirgin ruwa ya ritsa dasu a wannan yankin.Sai dai majiyar Sojin Amurkan na nuni dacewa wadannan hadura guda biyu ,basu da nasaba da aikin yan sari ka nike ko kuma makiya.
Har yanzu dai majiyar na nuni dacewa,ana kann neman sojin Amurka ukun da suka bace a hadarin,tare da agajin yansandan kasar Iraki. A hannu guda kuma wani mutumin Iraki ya gamu da ajalinsa lokacin da tashin Bomb ya ritsa dashi,ayayinda yake sauka daga motar Pasinja a birnin Bagadaza.Tashin bomb din ya lalata Bus din,ayayinda sauran pasinjoji 3 dake suka samu raunuka.A jiya lahadi kuwa yansandan Iraki 4 dake binciken motoci akan titin garin Ramadi dake yammacin Bagaza ne suka rasa rayukansu,ayayinda wasu yan bindiga dadi dake wucewa a mota suka buda musu wuta.
Hadarin jirgin yakin na Amurka na jiya dai ,na mai zama na biyar irinshi da Amurekan tayi asara a wannan wata da muke ciki kadai.Uku daga cikinsu yan yakin sunkuru suka harbo,ayayinda ranar jumaa guda ya fadi a Mosul jim kadan da tashinsa,inda ya kashe matukansa guda biyun,saannan gana jiya a Tigris.Amma har yanzu Amurkawan basu sanar dalilan faduwan jiragen na karshen mako ba.Wadanda suka ganewa idanunsu sun sanar dacewa jirgin ya fado ne sakamakon harbin rokoki da gurneti a garin na Mosul.
Wannan asara da Amurka tayi daga faduwan jiragen,ya dada jefa ta cikin halin ni yasu,ayayinda ake shirin mika mulki wa gwamnatin farar hula a Iraki a ranar 1 ga watan yuli.Batu da har yanzu ke fusakantar adawa daga babban limamin yan Shiyya Ayatullah Ali al-Husseini al Sistani,wanda ke bukatar zabe kai tsaye.
Jamian Amurkan dai sun bayyana cewa hali na rashin tabbas dangane da tsaro da Irakin ke ciki zai dada jinkirta gudanar da zabe a wannan kasa,ayayinda ahannu guda babu yadda Amurkan zatayi watsi da matsayin limamin yan Shiyyan,kasancewarsu lashi 60 daga cikin dari na adadin mutanen Irakin million 25. A wannan makon ne ake saran Sakatare general na MDD Kofi Annan zai sanar da matsayin hukumarsa dangane yiwuwan tura ayarin kwararru wadanda zasu fayyace halin da Irakin ke ciki dangane da shirin zabe kamar yadda Amurka ta nema. A ranar jummaaar data gabata ne babban jamiin binciken makamai na Amurka a Iraki david Kay yayi murabus daga mukaminsa,inda yace babu alamun cewa Iraki na mallakan wadannan makamai da Shugaba Bush ke zargi,kuma hakki ya rataya a Wuyan Shugaban na Amurka nayi alumman duniya bayani kann wannan batu.Ayayinda yan adawa musamman daga jammiyar Democrate na Amurkan ke zargin gwamnatin Bush tare da mataimakinsa Dick Cheney dangane wadannan makaman da suka bace,tare da bukatan ayi bincike,saboda sunyi amfani da karya wajen tabbatar da dalilansu na jagorantan yaki a Iraki.
 • Kwanan wata 26.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmM
 • Kwanan wata 26.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmM