1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraki.

May 12, 2004

Muqtad al-sadr yayi taron manema labarai.

https://p.dw.com/p/Bvjg
Cigaban tashin hankali a kewayen Najaf.
Cigaban tashin hankali a kewayen Najaf.Hoto: AP

A karo na farko bayan yakin fito na fito tsakanin fitaccen Limamin yan Shiyya da magoya bayansa,daya dauki wata guda yana gudana a yankin Najaf da kewaye,ya gudanar da taron manema labaru.Muqtad al-Sadr dai ya kwatanta halin da ake ciki na dauki ba dadi a Karbala da yakin Vietnam,inda ya jaddada cewa magoya bayan nasa su cigaba da afkawa sojojin taron dangin.Yace babu wani dalili dazai sa a samu sulhuntawa da Dakarun taron dangin,kuma kada mayakan nasa su yarda a gurbata musu wuraren Ibadunsu dake wadannan garuruwa masu tsarki.

A yau ne dai tankunan yakin Amurka tare da kariyar jiragen yaki kirar saukan ungulu,sukayi fadan fito na fito da magoya bayan Sadr a kusa da masallacin dake Karbala.A wannan arangama dai an ruwaito cewa yan ta kifen 25 suka rasa rayukansu,ayayinda aka rusa gine gine da dama,ata bakin sojojin taron dangin.

Da aka tambayeshi na iya lokacin da mayakansa zasu cigaba da gwabzawa da sojin taron dangin,Al-Sadr ya tunatar musu da yakin Vietnam,inda ya kara da cewa Iraki kasarsu ce ,kuma sunyi imani da Allah madaukakin Sarki,don haka suna da dama na yaki har sai sun ga karshen Amurka da kawayenta ,fiye da yadda ya kasance a Vietnam,kuma da yardar Allah hakarsu zata cimma ruwa.

Wannan dai na zama karo na farko da Limamin yan shiyyan da amurka ke fako ya bayyana a kafofin yada labaru,cikin tsukin makonni 4 da mayakansa Al Madhi suka dauki kayan fada domin kalubalantar amurka da kawayenta.

Al Sadr dai ya fadawa manema labaru cewa Amurka na yaki da addinin Islama ne amma ba kungiyoyin yan ta kifen Irakin ba,inda ya bada misalin yadda sojin Amurka da Britania ke azabtar da yan Irakin dake tsare a gidan kurkukun Abu Graib da makamantansu a Irakin.Sadr yace idan gaskiya ne Amurka tazo ceton alummar Iraki daga mulkin danniya na Sadam Hussein,da bazata bari a jefa talakawa bayin Allah cikin irin yanayi da suke cigaba da kasancewa a halin yanzu haka ba.A dangane da hakane yace babu gudu ba ja da baya,wajen cigaba da afkawa amurkan da kawayenta,sai dai abu daya da zaisa su janye shine,idan manyan shugabannin shiyyan sun bukaci haka.

To a hannu guda kuma batu daya fi daukan hankalin masharhanta a yau shine fille kann BaAmurken nan Nicholas Berg,da wadansu yan ta kife da suka sace shi sukayi.A wani kassete na Vedio da aka yayata a kafofin yada labaran kasashen Larabawa,an nuna Berg a tsugune a gaban wasu mutane dake sanye da bakaken tufafi,wadanda suka dauke kansa da wata doguwar wuka,wadanda sukace sunyi hakan ne a matsayin ramuwar gayya dangane da bakar Azaba da Prisononin Iraki ke fuskanta daga Sojin Amurka da Britani a kasar ta Iraki.

Fitattun gidajen talabijin na Aljazeera da Al Arabiyya,sun bayyanawa duniya hotunan yan ta kifen guda biyar da Dan kwangilan Amurkan a tsune gabansu,kafin su dauke kansa.Ayanzu haka dai kafofin yada labaru na cigaba da nuna hotunan,ciki harda hoton gangan jikin mutum,babu kai.

To sai dai Britania tayi Alla wadan wannan kisan gilla ta hanyar fille kai,da yan ta kifen da aka danganta da Al qaeda sukayi wa wannan BaAmurke.A wani taron manema da ya gudana a London,kakakin Tony Blair yace yace wannan mummunan yanayi ne wanda bazaa iya kwatanta shi da komai.

Tun a tsakiyar watan Afrilu nedai Dan kwangilan na Amurka Berg mai shekaru 26 da haihuwa ya bace,a kasar Iraki inda yake aiki.Wannan kisan gilla dai ya girgiza fadar gwamnatin Amurka ta White House,inda kakakinta ya lashi takobin cewa tabbatar da ganin cewa an gano wadannan yan ta kifen,tare da hukuntasu.

ZAINAB AM ABUBAKAR.