HALIN DA AKE CIKI A IRAKI. | Siyasa | DW | 02.12.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAKI.

Har yanzu dai kasar Iraki na cigaba da fuskantar tashe tashen hankula ,duk da cewa aski yazo gaban goshi dangane da zaben kasa baki daya da ake kyautata zaton zai gudana a ranar 30 ga watan janairu,kamar yadda mdd ta tsara

Birnin Bagaza,fadar gwamntin Iraki.

Birnin Bagaza,fadar gwamntin Iraki.

Wayewan garin yau,mutum guda ya rasa ransa kana wasu 11 sun samu raunuka sakamakon harin rokoki da aka harbawa wani yanki dake tsakiyar birnin bafgadaza.

Wadanda suka ganewa idanunsu hadarin dai sun bayyana cewa an harba wadannan rokokin ne zuwa wani gida da ake kann aikin gininsa a yankin karrada,dake bagadaza,wanda ya kashe daya daga cikin maaikatan tare da raunana wasu 11.

Bugu da kari an samu fashewa wasu makamai masu kama da Bomb a kusa da yankin Green zone dake dauke da jamian diplomasiyya na ketare da kuma na gwamnatin rikon kwaryar wannan kasa.To sai dai babu rahotanni dangane da sakamakon kai wannan hari.

Bugu da kari wasu mutane biyu sun samu raunuka daga harin da wasu yan bindiga dadi suka kai musu a garin Baquba dake areawacin Iraki,inda kuma ke zama garin wani tsohon general na rusashiyar gwannatin Sadam Hussein,Iyad Ibrahim al-Karawi.A hiran dayake da kamfanin dillancin labaru na AFP,Dan general din wanda kuma ya samu rauni daga wannan harin Mohammaed al-karawi,yace kimanin mutane 20 dauke da bindigogi ne suka afkawa gidan nasu,inda bayan fafatawa da masu tsaron gidan shi da danuwan mahaifinsa suka samu raunuka.

Tun dai a ranar 27 ga watan Nuwamban ne aka sace kanwarsa mai shekaru 15 da haihuwa,kuma ya zuwa yanzu babu labarinta ,balle na wadanda suka sace ta.kazalika an sace wani jamiar gunduwar Salahuddin ,Damaher Shaker Sudani a kusa da garin Baiji,da safiyar yau tare da jamian tsaron ta guda biyu,ayayinda yan bindiga dadi sukayiwa ayarinta kwanton bauna.

Sai dai conel Jassem Juburi na rundunanr yansandan Tikrit,ya fadawa yan jarida cewa,jamian tsaro na zargin wata kungiyar yan tarzoma da suka lashi takobin ganin bayan dukkan jamian gwamnati dake wannan yanki,dake zama mahaifar Sadamm Hussein.

A can garin Baiji kuwa wamni dan kunar bakin wake ya tayar da bomb motar dayake tafiya ciki inda ya bakunci lahira tare da wani mutum guda,kusa da cibiyar bincike na jamian tsaro dake garin,wanda ke yammacin kasar ta Iraki.

To sai dai ayayinda premier Iraki Iyad Allawi yake kann hanyarsa ta ziyaran kasashen Turai ayau domin neman goyon bayansu wajen zaben kasar dazai gudana a watan gobe,Amurka ta sanar da shirin ta na dada bunkasa dakarunta a Irakin domin tabbatar da tsaro ingantacce.

Alkaluma na nuni dacewa zaa kara dakarun na Amurka daga dubu 138 zuwa dubu 150nan da farkon watan janairu.A ziyar daya kai zuwa kasar Canada Shugaba Bish ya sake gabatar da hujjjojinsa na afkawa wannan kasa da karfin soji,tare da kira ga kasashen duniya dasu taimaka wajen sake ginin Irakin.

Allawi dai na kann hanyarsa zuwa Jamus da Rasha ,kasashe biyu daga cikin wadanda sukayi adawa da mamayar da Amurka tayiwa kasar a bara.Wannan Ziyara ta Premier Irakin zuwa Moscow da Berlin dake zama na farkon irinsa tunda ya haye karagar mulki watanni 6 da suka gabata,zai maida hankali ne wajen tattauna batun tattalin arziki.

 • Kwanan wata 02.12.2004
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveK
 • Kwanan wata 02.12.2004
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveK