1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Iraki

Zainab A MohammedAugust 16, 2006

Rikici ya barke a birane biyu mafi girma a kasar Iraki,kana bomb ya kashe mutane 8, da safiyar yau a birnin Bagadaza,batu dake dada dasa ayar tambaya a dangane da kokarin da dakarun Amurka dana Irakin keyi na samar da zaman lafiya a wannan kasa mai fama da rikici.

https://p.dw.com/p/Btyh
Tashin bomb a iraki
Tashin bomb a irakiHoto: AP

Gungun mayaka dauke da makamai sunyi arangama da dakarun Irakin na sama da saa guda a Basra,wadda ke zama birnin mafi girma na biyu a kasar,wanda kuma ke kasancewa garin da prime minista Nuri al-Maliki ya kafa dokar ta baci watanni biyu da suka gabata.

Yansanda sun sanar dacewa sun kashe mayakan sakan guda 6,a garin mosul mai tazarar km 390 arewacin bagadaza,garin dake fama da rigingimu na addini ,inda kuma sojojin Irakin dana Amurka sukayi ta dauki ba dadi da mayakan sakai na tsawon kwanaki 10,kafin asamu lafawan lamura.

Jamian Amurka dai sunyi gargadin cewa,idan ba matakan tsaro aka karfafa ba,Irakin zata fada yakin basasa.A makon daya gabata dai an tura karin dubban dakarun Amurkan zuwa cikin Bagadaza,domin samarda da tsaro a unguwanni da ake samun yawan tashin hankali.

Washinton dai na mai raayin cewa,fadar gwamnatin kasar itace kann gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar baki daya.Duk da alkawarin da gwamnati mai ci a yanzu ta dauka na sasanta kann bangarori dake gaba da juna a Irakin,watanni uku bayan rantsar da gwamnatin da yan shia kewa jagoranci,akarkashin prime minista almaliki,ana cigaba da fuskantar tashe tashen hankula.

Ayau din dai tarwatsewar wani bomb a wata karamar kasuwar gwanjo dake gabashin Bagadazan, ya kashe mutane 8,kana ya raunana wasu 28.

Mohammed Karin daya ganewa idanunsa,yace bomb din ya ritsa da rayukan bayin Allah ne wadanda suka zo wannan kasuwar gwanjo domin sayen kayayyakin da suke bukata na yau da kullum.Yace wani tsoho da yayansa guda biyu nan take suka gamu da ajalinsu.

Dan jaridan kanfanin dillancin labaru na Reuters a Basra ,yace wannan harin bomb ya biyo bayan harin da aka kaine a ofishin gwamna dana majalisar zartarwar Basran.

Aqil al-furaiji,daga jammiyar yan shgia dake mulki a Irakin yace wani jamiin dan sanda ya gamu da ajalinsa,ayayinda wasu 5 suka jikkata.

Kakakin rundunar sojin Britani dake Basra,Major Charlie Burbridge yace an tura karin soji guda 100,domin tallafawa dakarun iraki,dake fafatawa da sojojin sakan..

Wadannan tashe tashen hankula da wadannan yankuna suka wayi gari cikinsa ayau dai,ya biyo bayan fadan daya barke ne jiya a wurin ibada na kerbala a jiya ,tsakanin dakarun sojin iraki da magoya bayan limamin yan shia.

Sanarwar maaikatan tsaron Iraki a yau na nuni dacewa mutane 12 ne suka rasa rayukansu a wannan fada na jiya a kerbala,wadanda suka hadar da yansanda biyu.

Dubban yan darikar shia dake goyon bayan sheikh Mahmoud al-hasani ,nedai sukayi zanga zanga a garin hilla,inda suke bukatar a saki mutane kusan 300,shiawa da aka cafke a rikicin na jiya.