1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A HAITI

ZAINAB AM ABUBAKAR.March 10, 2004
https://p.dw.com/p/BvlP
Staff Sergent Timothy Edward mai magana da yawun dakarun, ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa sojojin Amurkan sun budawa mutane wutane a ayayinda yan bindiga dadin ke kokarin bude wuta a kusa da gidan Prime ministan mai barin gado.Wannan ya kasance karo na uku kenan da Sojojin Amurkan suka bindige mutane cikin kwanaki uku kachal.A ranar lahadi ne suka bindige wani dan bindiga dadi daya budawa masu zanga zanga wuta,ayayinda ranar litinin suka bindige wani Direba a yayinda ya doshi wajen binciken jamian tsaro na kann titi ba tare da ya rage gudu ba.

Edward yace Sojin Amurkan na sintiri ne a kusa da gidan Prime ministan mai barin gado Yvon Neptune,lokacin da aka buda musu wuta ,nan take suka mayar da martani inda suka harbe mutane 2 har lahira.A daren jiya ne kuma wasu mutane suka budawa ayarin na Amurka wuta,inda nan take suka mayar da martani.To sai dai tuni hukumar tsaron Amurka ta kare wannan harbi da sojin sukayai,dacewa suna aiki ne bisa umurni da aka basu nacewa idan har anyi musu barazana su mayar da martani.

Wannan harbe haben yazo ne a dai dai lokacin da sojojin kiyaye zaman lafiyan ke shirin karban makamai daga mayakan kasar,abunda ake gani zai kasance mawuyaci bayan rikicin siyasa daya dauki makonni yana gudana a Haitin.Magoya bayan tsohon shugaba Jean Bertrand Aristide a jiya sun bayyana rashin jindadinsu dangane da nadin Gehard Latortue a matsayin sabon Prime ministan Haitinsabon Prime ministan ya kasance mai sukan lamirin sHugaba Aristide,wanda kuma keda zama a Miami.

Masu lura da alamura dakaje suzo na ganin cewa bazai iya rike wannan mukami ba ,tunda baya zama a wannan kasa.Latortue,wanda ya kasance tsohon jammin MDD ,wanda kuma ya riki mukamin ministan harkokin waje,zai fuskanci matsaloli wajen samar da zaman lafiya ,a wannan kasa dake yankin Carrebean,wadda ta fuskanci rikicin yan tawaye daya kori Shugaba Aristide ranar 29 ga watan daya gabata.Aristide ya fice daga wannan kasa ne bayan yan tawayen sun kwace Rabin kasar ,ayayinda sama da mutane 400 suka rasa rayukansu.

To sai dai rahotanni daga kasar Afrika ta kudu na nuni dacewa kungiyar gamayyan Afrikance zata yi shirin mafaka na lokaci mai tsawo wa tsohon shugaban na Haiti,da a halin yanzu haka ke birnin Bangui din Afrika ta tsakiya.Tawagar Afrika ta kudu a karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin waje Aziz Pahad,sun gana da Shugaba Aristide,inda suka tattauna yanayin daya jagoranci ficewansa daga Haiti zuwa Afrika.Kungiyar ta AU dai mai wakilai 53 ta bayyana cewa ficewan shugaban na Haiti babban barazanace wa makomar Democradiyya.A inda Kasar Afrika ta kudun ta hade da kasashen yankin Carebean wajen kira da gudanar da bincike kann batun tsohon shugaban na Haiti ,wanda yace Amurka ce ta tilasta masa barin mukamin nasa.