1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Habasha bayan rasuwar mutane sama da ashirin

ibrahim saniJune 9, 2005

Da alama dai a iya cewa zaben yan majalisun dokoki da akayi a Habasha shine makasudin tsunduma kasar a cikin hali na rudani a yanzu haka

https://p.dw.com/p/BvbR

To ya zuwa yanzu dai bayanai daga kasar ta habasha na nuni da cewa gwamnatin kasar ta bayar da umarnin yiwa shugaban jamiyyar adawa ta kasar tsaro na talala a gidansa bisa hasashen cewa shine yake kara rura wutar rikice rikice a kasar.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa gwamnatin ta zargi jamiyyar adawa ta CUD ne da ingiza wutar rikice rikice na nuna rashin kin yarda da sakamakon zaben yan majalisun dokoki da aka gudanar a kasar a watan daya gabata,duk kuwa da cewa hukumar zaben kasar ta dakatar da bayar da sanarwar cikakken sakamakon zaben.

Jamiyyar adawa ta kasar dai wato CDU ta zargi gwamnatin kasar ta habasha ne da gudanar da magudi a lokacin zaben yan majalisun dokokin a kokarin da take na yin ta zarce a gadon mulkin kasar.

Ire iren wadannan tashe tashen hankula kwanaki kadan bayan zaben yan majalisun dokokin a yanzu haka yayi sanadiyyar rayukan mutane 26.Hakan kuwa ya biyo bayan wata arangama ne da akayi a tsakanin masu zanga zangar da kuma jamiian tsaro a inda nan take jamian yan sanda suka bude musu wuta wanda hakan ya janyo asarar wadan nan rayuka da muka ambata a sama.

Game da wannan arangama data wanzu kuwa a ranar larabar data gabata,a yanzu haka rahotanni daga kasar na nuni da cewa da yawa daga cikin mazauna birnin Addis Ababa na cike da shakku da kuma dari darin abin da kaje yazo na hasashen ballewar wata rigimar.

Bisa hakan kuwa tuni gwamnatin kasar ta umarci jamian tsaro dasu dinga yin sintiri a manya manyan titunan kasar don tabbatar da tsaro da oda ko hakan ya kawo kwanciyar hankali a zukatan al,ummar birnin.

A daya hannun kuma game da wannan mataki da gwamnatin kasar ta Habasha ta dauka a kann yan jamiyyun adawar tuni kungiyyar tarayyar Turai wato Eu tayi Allah wadai dashi da cewa bai dace ba ko kadan.

A cewar babban jamii na kungiyyar daya jagoranci tawagar masu sa ido game da zaben wato Ana Gomez ya kara da cewa tsaro na talala da akewa shugaban jamiyyar adawar da cin mutunci da wulankaci da akanyi akan wasu yan jamiyyar adawar abune da zai kara dagula al,amurran siyasar a wannan kasa, a don haka akwai bukatar da ayi karatun mun natsu.

A wata sabuwa kuma gwamnatin kasar ta Habasha ta haramta aikin wasu yan jaridu bakwai ciki kuwa har da wakilan tashar DW guda biyu wadanda ke aikowa sashen harshen amaric rahotanni daga kasar ta Habasha, hakan ala tilas yasa wakilin na Dw ya dawo izuwa Gida.

Dalilin daukar wannan mataki daga bangaren gwamnatin kasar kuwa shine wai suna aiko da rahotanni dake da son rai a cikin su,to sai dai a waje daya kuma rahotanni daga kasar sun shaidar da cewa kusan dukkannin motocin taxi taxi dake aikin sufuri a birnin Addis Ababa sun kawata motocin su da kananan rediyoyi masu gajeren zango domin kama tashar ta Dw sashen harshen Amaric,saboda ta kanta ne kawai suke samun sahihin labaran abubuwan dake gudana a kasar su ba tare da an tace ba.