1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Gaza

Babangida JibrilJanuary 5, 2009

Dakarun Izraela na cigaba da Lugudan Wuta a Zirin Gaza

https://p.dw.com/p/GSV1
GazaHoto: AP

A yayinda Israila keci gaba da kai hare hare a yankin zirin Gaza wanda kuma ke haifa da mutuwan fararen hula musanman mata da yara, ƙungiyar arayyar Turai da sauran ƙasashen Duniya naci gaba da kira ga Israila da Ƙungiyar Hamas dasu tsagaita wuta, domin samun damar kai kayan agaji yankin.

Firaministan ƙasar Czech da yanzu haka ƙasar sa ce ke shugabantar Ƙungiyar Taraiyar Turai ta EU Mirek Topo-lanek, yace yana kokarin ganin a kalla an samu wata yarjejeniya da zata samar da tsagaida wuta a zirin na Gaza.

Sai dai kuma Firaministan wanda ya sanar da hakan a wani taron manema labarai, bai bayyana hanyoyin da yake shirin ɗaukan ba. Koda yake yace ya tattauna da Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel da Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan ,kuma yana shirin tuntuɓar shugaban Amurka mai barin gado George W. Bush da Firaministan Israila Ehud Olmert a yau litinin.

Wannan labari kamar yadda yace "yafi karfin ƙungiyar Tarayar Turai ita kaɗai. A kwai bukatar tuntuɓar dukkan ɓangarorin da rikicin ya shafa kai tsaye, da ma wayanda rikicin bai shafa ba kai tsaye domin shawo kan rikicin.

Da yake jawabi a wajen wani taron neman zaman lafiya da aka gudanar da ƙasar Masar ministan harkokin wajen ƙasar (Checks) Karel Schwarzenberd ya kara da cewa.

Karel Schwarzenberg Außenminister Tschechien
Karel SchwarzenbergHoto: picture-alliance/ dpa

"Mun gana da takwara ta ministan harkokin Wajen israila Zipi Livni. Ganawa ta keke da keke inda muka gabatar mata da bukatar ƙungiyar EU na tsagaita wuta cikin hanzari tare da dakatar da harba rokoki akan Israilan..."

A ganawar da wakilan ƙungiyar ta Tarayyar Turai suka yi da Shugaban Masar Hosni Mubarak litinin ɗinnan kafin ya gana da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy, Babban Jami'in Harkokin wajen ƙungiyar Javier Solana ya jaddada fatan ganin Israila da hamas sun tsagaita wuta.

"Muna fatan ganin samun tsagaita wuta cikin gaggawa, kuma domin samun nasarar hakan zamu ci gaba da aiki tare da samun goyon bayan ƙasar Masar".

Solana im Iran
Javier SolanaHoto: AP

A yayin da ƙasashen Duniyan ke kaiwa da komawo domin kawo ƙarshen wannan bala'i, ƙasashe da dama naci gaba da mika taimakon agaji zuwa Palastinu dake cikin wani hali na kaka nikayi a sabili da lugudan wuta da Bani Israilan keyi masu.

Ƙasar jamus ta ware Euro miliyan 11 a wannan wata domin sayan kayan jin kai ga al'uman na Palastinu.Kakakin Ma'aikatar harkokin waje Jens Ploetner wanda ya sanar da hakan a Berlin yace za'a baiwa ƙungiyoyin jin kai wa'yannan kuɗaɗe domin sayo taimako ga jama'ar da suka jigata.

A yayin da ƙasar Sweden ta ware kusan Dala miliyan 2 domin sayan kayan agaji a Asibitoci da kuma samar da magunguna.

Jama'a da dama ne dai ke ci gaba da gudanar da zanga zangar lumana a ƙasashen duniya daban-daban,waɗanda ke Allah wadarai da ƙasashen Turai da Amurka da Masar da ake zargin su da marawa israila baya a wannan yaƙi da takeyi da ƙungiyar Hamas.

Rahotannin dake fitowa daga yankin yanzu haka na cewar a kwanaki 10 da Israilan ta kwashe tana ɓarin wuta a yankin na Gaza, a kalla Palastinawa 517 ne suka rasu, ciki kuwa harda Kananan yara 87 kana wasu fiye da 2500 kuma suka samu raunuka.