Halin da ake ciki a Gaza | Labarai | DW | 10.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Gaza

Kungiyar tarayyar turai ta baiyana damuwa da halin da jamaá ke ciki a Gaza tare da yin kira ga Israila ta bayar da dama domin kai kayan agaji zuwa yankin. Kungiyar ta kuma zargi Israila da yin amfani da tsauraran matakai soji wadanda ke kara jefa alúmar Palasdinawa a Gaza cikin mawuyacin hali. Israilan dai ta sanar da cewa za ta cigaba da kai farmaki Gaza har sai abin da hali ya yi domin matsawa yan takifen dake tsare da sojin ta su sako shi. A halin da ake ciki an sami karuwar tashe tashen hankula a yankin zirin Gaza bayan da a daren jiya wani jirgin saman Israila ya kai hari a kann wasu yan gwagwarmayar Palasdinawa inda a kalla mutum daya ya rasa ran sa yayin da wasu mutanen uku suka jikata. Sojin Israila sun bayana mutanen da cewa yan takife ne na kungiyar Hamas wadanda ke shirin harba rokoki zuwa cikin Israila.