1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Gaza

A cigaba da rikicin zirin Gaza kuwa,akalla Palasdinawa 6 ne suka rasa rayukansu a somame da Izarela ke cigaba dayi,da suna neman yan yakin sunkurun kungiyar hamas.Rundunar sojin kungiyar ta hamas dai,ta karyata sanarwar da Izraela tayi ,na raunana shugaban rundunar Mohammed Dief.Hare haren jiragen saman Izraelan ya lalata wani gida a gaza. Daga cikin mutane guda shida da suka rasa rayukansu a gazan kuwa,biyu yara ne kanana.Tun da asubahin yau nedai motocin yakin yakin Izraelan suka kutsa tsakiyar gaza.Tun makonni biyu da dakarun Izraelan suka kutsa gazan,sakamakon cafke sojinsu guda dai,sun lalata gine ginen gwamnati da gidajen jamaa,ayayinda mutane 65 suka kashe,banda wadanda suka jikkata daga wadannan hare hare,ta kasa da kuma sararin samaniya.

 • Kwanan wata 12.07.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6E
 • Kwanan wata 12.07.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6E