1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A GARIN NAJAF.

Maryam L.Dalhatu.August 11, 2004
https://p.dw.com/p/BvhP

Yan kasar iraqi,a yau sun bayyanawa prime ministan kasar mai rikon kwarya Iyad Allawi bukatar su ta neman ya tsawatar akan fadan da aka dauki kwanaki bakwai ana gwabzawa tsakanin shiawa da kuma sojin amurka a garin najaf.

Su dai bukatar su shine Iyad Allawi,ya samar da matakan wanzar da zaman lafiya a duk fadin kasar,domin kuwa a halin da ake ciki,babu kwanciyar hankali,musamman ma yadda wannan rikici na najaf ke dada kazanta.

A cewar wani jamiin maaikatar ilmin kasar wanda ya bada sunansa Abu Saad,kamar yadda ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na reuters cewa Mr Allawi na bakin kokarin sa akan kawo karshen tashe tashen hankula a kasar ta iraqi.

Wannan rikici ya kasance mafi tsawo a duk rikice rikicen da sukai ta faruwa a kasar tun bayan da amurka ta mika mulki hannun yan kasar.haka kuma ya zama wani babban kalubale ga wannan gwamnati ta Iyad Allawi.

Shi dai Mutadr Sadr shugaban shiawan kasar iraqi,yayi kira ga magoya bayansa da su cigaba da yakar sojin amurka koda bayan ransa ne,har sai inda karfinsu ya kare ko kuma suka rasa rayukansu baki daya.

Wannan rikici dai na najaf,a yanzu ya janyo an fara wasu tashe tashen hankulan a wasu garuruwan daban daban kamar birnin bagadaza,amara,basra da sauransu.

A yayin da wasu ke ganin matakin da Iyad Allawi ya dauka na hana shiawa yakar amurkawan shine daidai,wasu suna ganin cewa bai kamata ya bar amurkawan su cigaba da yakar shiawan ba,idan har amurkawan sun daina mai da martani zai kasance babu wanda shiawan zasu yaka,hakan kuma shi zai kawo karshen wannan rikici kamar yadda mutanen garin suka bayyana.

Shi dai Saber Ali daya daga cikin mutanen da suka tattauna da kamfanin dillancin labaru na reuters cewa yayi har yanzu basu ga wani mataki da gwamnatin kasar ta dauka ba a kann wannan rikici.

Su dai a shawarar su kamata yayi a nemi sulhu da wadannan yan tawaye ba wai a ce zaa cisu da yaki ba.

Rahotanni daga maaikatun lafiya a kasar sun tabbatar da cewa tun da aka fara wannan rikici kawo yanzu mutane ashirin da biyu ne suka rasa rayukansu wasu dari da tara kuma suka jikkata a garin amara,haka kuma wasu mutane tara ne suka rasa rayukan su wasu ashirin da hudu kuma suka samu raunuka a garin basra.

A garin nasiriyyah kuwa mutane goma sha hudu ne suka rasa rayukansu wasu talatin da daya kuma suka samu muggan raunuka,banda kuma mutane da dama da suka rasa rayukan su a garin najaf.

A wata sabuwa kuma,a safiyar yau laraba a birnin bagadaza,wani bomb ne ya tashi a tsakiyar wata kasuwa,wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane shida tare kuma da raunana wasu mutane tara.