Halin da ake ciki a duniya bayan buga hotunan batanci ga Islam | Zamantakewa | DW | 08.02.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Halin da ake ciki a duniya bayan buga hotunan batanci ga Islam

Rikice rikice a game da hotunan batanci ga fiyayyen halitta da aka buga na neman gagarar kundila

default

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin musulman duniya nada raáyin cewa akwai munafunci a cikin dalilin da wasu jaridu na yamma suka bayar game da wannan batanci da akayiwa fiyayyen halitta, Muhammadu SAW.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa da yawa daga cikin jaridun yamma sun nunar da cewa an buga zane zanen batancin ne bisa yanci na fadin albarkacin baki.

To sai dai a hannu daya,babban magatakardar kungiyyar kasashen larabawa, wato Amr Moussa cewa yayi batu na yancin fadin albarkacin baki, bai ba da damar yiwa mutum ko addinin sa batanci ba. Ballantana,fiyayyen halitta MSA.

Shima dai Sheik Andel Aziz Al Qassim, daya daga cikin manya manyan malamai a Saudiya, cewa yayi yancin fadin albarkacin baki, bai bawa kowa damar yin batanci ga annabawa da addinin musulunci ba.

Da yawa dai daga cikin musulmai na daukar wannan abu daya faru a matsayin wata kafa da kasashen yamma suka yi amfani da ita don cin mutuncin addinin su na Islama,inda suka ba da misali da cece kucen daya wanzu a kasar Faransa dangane da dokar hana daura dankwali a hannu daya kuma da nuna shakulatin bangaro da kasashen yamma suka yi a game da nararar da kungiyyar Hamas ta samu a zabubbukan yan majalisun dokoki daya gudana a yankin.

Daga dai tun lokacin da aka buga hotunan batancin a watan daya gabata kawo yanzu musulmai da daman gaske ne daga kasashe daban daban na duniya, suke ci gaba da gudanar da zanga zanga don yin Allah wadai da wannan abu daya faru.

A wasu kasashen ma har da lalata ofisoshin jakadancin kasashen Denmark da Sweden da Norway a hannu daya kuma da kokkona tutocin kasashen.

Har ilya yau a wasu kasashen kuma, an bukaci kauracewa duk wasu kayayyaki da suka fito daga kasar ta Denmark, inda a nanne aka fara buga hotunan zane zanen batancin ga Fiyayyen halittar.

A wata sabuwa kuma, a yau laraba,wata jarida ta kasar Iran ta bukaci a samar da zane zane game da kisan kiyashi da akayiwa bani yahudu.

Ya zuwa yanzu dai a cewar bayanai daga kasar ta Iran wannan jarida ta dukufa ka´in da na´in wajen neman hotunan da suka dace da siffanta wannan abu daya faru da bani yahudun, a matsayin ramuwar gayya,bisa buga hotunan batancin ga addinin islama da kuma fiyayyen halitta.

Bisa kuwa wannan mataki da wannan jarida ke kokarin dauka, gwamnatin Jamus na mai ra´ayin cewa hakan ka iya fadada wannan rikici izuwa wani abu na daban a tsakanin Israela da duniyar musulmai.

A kuwa wani mataki na ganin an warware wannan matsala cikin ruwan sanyi, kasar Malaysia tace zata shirya wani taron kolin wuni biyu a tsakanin duniyar musulmai da kuma kasashen yamma, a wani yunkuri na fuskantar juna.

A cewar ministan harkokin wajen kasar, wato Syed Hamid ,tsohon shugaban kasar Iran wato Mohd Khatami zai kasance daga cikin mutane 60 da aka shirya zasu gabatar da jawabai a lokacin taron.

Daga dai cikin masu gabatar da jawaban, an shirya cewa rabi zasu zone daga kasashen turai da Amurka ragowar rabin kuma daga duniyar musulmai.

 • Kwanan wata 08.02.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTq
 • Kwanan wata 08.02.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTq