Halin da ake ciki a Darfur | Labarai | DW | 11.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Darfur

Jakadan mdd a Sudan Jan Eliasson ya bayyana cewar,dukkan wani jinkiri da aka samu wajen gudanar da tattaunawar sulhu tsakanin Khartum da yan tawayen Darfur,zai dada jefa yankin yammacin Sudan din cikin hali mawuyaci na karuwar tashe tashen hankula.Wannan gargadi nasa dai yazo ne bayan da kungiyar yan tawayen SLA dake Darfur ,tayi barazanar kauracewa tattaunawar sulhu da zaa fara ranar 27 ga wannan wata a kasar Libya.Kungiyar wadda ke daya daga cikin kungiyoyin dake fada a lardin na Darfur,tace zata halarci taron sulhun ne kadai idan an tura dakarun mdd ,domin tsayar karuwan asarar rayuka da akeyi a yankin,wanda aka dangana da dakarun gwamnatin Sudan din.