Halin da ake ciki a CHad bayan hare haren yan tawaye | Labarai | DW | 22.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a CHad bayan hare haren yan tawaye

Shugaban yan tawaye na Chad, Mohd Nur yace kungiyyar sa na shirye shiryen kaiwa bangaren gwamnatin kasar hari, bisa manufar kifar da gwamnatin shugaba Idiris Debby.

Mohd Nur, wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Reuters haka, yaci gaba da cewa harin da kungiyyar sa ta kai izuwa Adre a makon daya gabata, abu ne shiryeyye, a kokarin da suke don kifar da gwamnatin kasar.

Bisa hakan , shugaban adawa na kasar ya kara da cewa nan gaba kadan zasu kara kaddamar da wani sabon harin, amma yaki ya ambaci inda zasu kai harin a wannan lokaci, amma duk da haka yace watakila birnin N´Djamena.

A lokacin wannan arangama dai, yan tawayen sun shaidar da cewa sun rasa mutanen su tara ne kawai, wasu kuma biyu suka bace, amma sun samu galabar kisan sojin gwamnatin kasar 70.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ta Chad ta tabbatar da cewa wannan gari na Adre na hannun su, kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali sun fara wanzuwa a kasar.