1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Britania

Zainab A MohammedAugust 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bu64

Yansanda a Britania sun sanar da cafke mutane 24 da ake zargi da hannu a shirin kaiwa jAmurka hari,wanda jamian binciken Amurkan sukace kimanin jiragen sama 10,aka nufa da kai wadannan hare hare.

Bugu da kari jamian kasar Pakistan sun sanar da kame wasu mutane 7,akokarin su na tallafawa Britania wajen gano wadanda keda nufin kai wadannan hare hare.Yanayin sinadran da akayi niyyan kai wadannan hare hare dasu,na nuni dacewa yan taaddan na dada samun sabbin fasahu na kai hare hare,wa wuraren da suke muradi.A sakamakon wannan hali da ake ciki ne, Pasinjoji a filayen jiragen saman London ke fuskantar jinkiri,ayayinda ake cigaba da gudanar da bincike a dangane da wadanda keda hannu a yunkurin kai wadannan hare hare na taaddanci da sinadrai masu nasaba da ruwa.