Halin da ake ciki a Banghladash | Labarai | DW | 18.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Banghladash

Yini uku bayan mummunar guguwan nan ta Sidr a ƙasar Banghladash,jami’an agaji na cigaba da kokarin kai ɗaukin kayayyakin masarufi wa dubbannin waɗanda suka tsra da rayukarsu,bayan asarar gidajensu.Jami’an dai sun bayyana tsoron cewar zaa iya samun karuwar yawan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan guguwa ,zuwa 1,700 ko kuma fiye da hakan.A gunduwar Jhalokati kaɗai,kimanin ƙuyuka 500 ne suka salwanta.A yanzu haka dai jiragen soji kirar saukar ungulu,na cigaba da kai abinci yankunan da abunda ya shafa,ayayinda jamian sojin ruwa da jiragen ruwa sun fara kai ɗaukin abinci zuwa kauyuka dake gaɓar koguna.Tun a daren ranar Alhamis nedai kasar ta Banghladashi ta fuskanci bala’in iskar,dake tafiya nisan km 250 acikin sa’a guda.Kasashen turai dai sun bawa Banghladash taimakon euro million 1.500,ta fuskar agajin gaggawa,inda jamus tayi alkawarin karin dubu 500.