Halin da ake ciki a Australiya bayan zaɓe | Labarai | DW | 22.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Australiya bayan zaɓe

Jam'iyun Labour da Liberal sun fara zawarcin sauran jam'iyu na Australia da nufin ƙulla ƙawance da zai ba su damar kafa gwamantin haɗaka.

default

Firaminista Gillard ta Australiya

Manyan jam'iyun biyu da ƙasar Australiya ta ƙunsa sun fara zawarcin sauran jam'iyun da nufin ƙulla ƙawance da zai bai wa ɗayansu damar kakkange madafun iko. kiyasin baya-bayan nan ya nunar da cewa jam'iyun na Labour da ke rike da mulki, da kuma ta Liberal mai adawa ba za su samu rinjaye da zai basu damar kafa gwamnati ba.

A daidai lokacin aka kusa kammala ƙidayar ƙuri'un, jam'iyar Liberal da Tony Abbot ke jagoranta ne ke kan gaba da kujeru 73. Yayin da jam'iyar Labour da ke rike da mulki ke biya mata baya da kujeru 72. Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 70 da suka gabata da za a kafa gwamantin haɗaka a ƙasar ta Australiya.

Masharhanta na danganta rashin nasara na Firminista mai ci a yanzu wato Julia Gillard, da butulce wa tsohon Firaminista Rudd da ta yi watanni biyun da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu