Halin da ake ciki a ƙasar Iraqi | Labarai | DW | 24.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a ƙasar Iraqi

A ƙasar Iraqi an baiyana dokar hana zurga zurga jamaá da gwamnatin ta sanya wanda ya hana musulmi fita sallar Jamaá ta wannan makon da cewa ya taimaka wajen hana aukuwar wani tashin hankali a tsakanin yan shiá dana sunni. Kimanin mutane 200 ne aka ruwaito sun rasa rayuka su a birnin Bagadaza da kuma sassan kasar Iraqi a sakamakon harin da aka kai a wasu wurare ibada tsarkaka na mabiya shiá. A halin da ake ciki dukkanin tituna sun kasance fayau ba mutane sai dai a birnin Sadr yan shiá sun bujirewa dokar bayan da matashin malamin nan Moqtada al Sadr ya umarci magoya bayan sa da su fito sallar jumaá. A hudubar sa Sadr yana cewa musulmi ba maƙiyan juna bane, kuma dukkan musulmin da ya kaiwa dan uwa hari, to shi ba muslmin ƙwarai ba ne. Wani babban malami daga bangaren yan shiá Abdulaziz al Hakim ya ɗora alhakin hare haren da aka kaiwa masallaci a birnin samara da cewa aikin magoya bayan Saddam da zarqawi ne amma ba yan sunni dake cikin kasar Iraqi ba. A waje guda kuma ƙungiyar tarayyar turai ta yi Allah wadai da harin harin da aka kaiwa tsarkakan wuraren ibadar na yan shiá a kasar Iraqi.