Halin da ake ci a Burma | Labarai | DW | 28.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ci a Burma

An fadada dokar han afitan dare da aka kafa a kwanaki ukun da suka gabata a birnin Rangoon din kasar Burma.A dauki tsawon ranar dayau dai ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin masu zanga zangar muradin kafuwar Democradiyya da,a hannu guda kuma da jamian sojin kasar,wadanda keta harbin dubban mutanen da harsashin roba.Jamian Diplomasiyyan kasashen Australia da Sweden dai sun shaidar dacewa akwai akalla mutane 35 da suka rasa rayukansu a rikicin na yini uku,sabanin guda 9 da hukumomin kasar ta sanar.Shima sakatare general na mdd Ban Ki Moon ya bayayana damuwansa da halin da ake ciki akasar ta Burma.