1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da Afirka ke ciki a jaridun Jamus

Mohammad Nasiru AwalSeptember 12, 2003
https://p.dw.com/p/BvqY

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne kan ranar tunawa da hare-haren ta´addanci da aka kaiwa Amirka. Amma duk da haka wasun su sun waiwayi nahiyarmu ta Afirka a rahotannin da suka buga. A sharhin da ta rubuta wanda ta yiwa taken har yanzu ana ci-gaba da fada a Liberia, jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa makonni 3 bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da ´yan tawaye, har yanzu babu alamar zaman lafiya a wannan kasa. Jaridar ta labarto cewa a ´yan kwanakin da suka wuce an gwabza wani kazamin fada a wani wuri mai tazarar kilomita 50 daga birnin Monrovia. Wannan fada dai shine mafi muni tun bayan amincewa da yarjejeniyar zaman lafiyar. Ko da yake rundunar kiyaye zaman lafiya ta ECOWAS da aka girke a Liberia ta ce ta shawo kan wannan lamari a garin Kakata, amma har yanzu kungiyoyin ba da agaji a Monrovia sun rasa yadda zasu yi su mayar da ´yan gudun hijira kimanin dubu 400 zuwa yankunansu na asali. Ita kuwa a nata sharhin jaridar Frankfurter Rundschau ta rawaito wani kakakin rundunar kiyaye zaman lafiya na cewa wata tawagar sojin jamhu´riyar Benin ta isa Monrovia, abin da ya kawo yawan sojojin kasashen Afrika Ta Yamma dake Liberia yanzu ya kai dubu 3 da 250. A kuma halin da ake ciki sojojin Nijeria sun isa garin Salala yayin da na Guinea-Bissau kuma suke kan hanyar zuwa garin Totota. A wani labarin kuma jaridar ta FR ta rawaito jami´an hukumar lafiya ta duniya na cewa sama da mutane dubu 6 sun kamu da cutar kolera a Liberia. Ita ma jaridar Tageszeitung ta yi sharhi game da sojojin na Afrika Ta Yamma da aka girke Liberia, tana mai cewa yanzu haka an tura dakarun zuwa wajen birnin Monrovia. Jaridar ta ce yanzu haka dai sojoji 600 daga kasar Guinea-Bissau sun doshi hanyar garin Totota inda kimanin makonni 2 da suka wuce aka fafata tsakanin sojojin gwamnati da na ´yan tawaye, wanda hakan ya janyo kwararar ´yan gudun hijira sama da dubu 50.

A wani labarin kuma jaridar ta TAZ ta rawaito sassaucin da Faransa ta nuna dangane da dagewa Libya takunkumin karya tattalin arziki da MDD ta kakaba mata. Jaridar ta jiyo ministan harkokin wajen Faransa na cewa sun cimma daidaito da gidauniyar Gaddafi game da kudin diyya da za´a ba iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama kamfanin UTA a Nijer a shekarar 1989. Ita ma jaridar FAZ ta yi sharhin akan wannan batun inda ta fara da cewa yanzu Faransa ta janye adawar da ta nuna na dage wannan takunkumi akan Libya. Jaridar ta ce Faransa ta canza shawara ne bayan da iyalan mutane 170 da suka mutu a wannan hatsari suka amince da diyyar da Libya zata ba su. Jaridar FR kuwa cewa ta yi yanzu an share fagen dagewa Libya takunkumin MDD. Ko da yake Libya ba ta amsa laifin hannu a ta da bam din da ya tarwatsa wannan jirgi ba, amma ta amince ta ba da diyya ta kudi dala miliyan 34.

Yanzu kuma sai kasar Ghana inda jaridar FR ta rawaito cewa ana shirin mayar da kananan yara sama da dubu daya da aka bautar da su zuwa ga iyayensu a kasar Ghana. Su dai yaran, wadanda aka tilasta musu yin kwadago a yankin masunya dake kusa da kogin Volta na kasar Ghana, an sake su bayan da wata kungiya da ke kare ´yancin kananan yara ta yi alkawarin taimakawa masunyan a rayuwar su ta yau da kullum. Yaran da yawan su ya kai 170 yanzu haka suna kan hanyar komawa gida. Kana kuma an kiyasce cewar akwai kananan yara da yawan su ya kai dubu 3 dake aikin bauta a wannan yanki na kasar Ghana. Bari mu kammala shirin da kasar Kenya inda tsohon shugaban kasa Daniel Arap Moi ya sauka daga kan mukaminsa na shugaban jam´iyarsa ta KANU. Jam´iyar wadda ta mulki kasar tsawon shekaru 24 a karkashin Moi, ta sha kaye a zaben shugaban kasa da ya gudana a cikinwtan dessamban bara.

To jama´a karshen shirin kenan na Afirka a Jaridun Jamus.