1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da a ke ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Yahouza sadissouSeptember 5, 2005

A kasar Iraki a na ci gaba da gumurzu tsakanin yan yakin sunkuru da dakarun Amurika. Akai alamun cimma daidaito tsakanin Isra´ila da Palestinu a game da zirga zirga a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/BvZu

ar Iraki, kwanaki kadan kamin zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar, hare haren kunar bakin wake na cigaba da wakana a sassa daban daban.

A sahiyar yau, kussan mutane 30 ne dauke da makamai, su ka yi lugudan wuta, a gidan ministan harakokin cikin gida, dake birnin Bagadaza.

Opishin yan sanda ya bayana cewa, maharai sun zo kan tawagar motoci fiye da 10, shake da manyan makamai.

A cuikin harbe-harben kan mai uwa da wabi, sun hallaka jami´an tsaro 2, masu gadin gidan ministan, to saidai minstan ya ketara rijiya da baya.

A hannu daya kuma,sojojin Amurika 4, da yan fara hulla 3, na Iraki sun ji mumunan raunuka, a wasu hare haren gurneti, na daban, da su ka wakana a Bagadaza.

Jim kadan,bayan wannan hari, a yammacin baban birnin Irakin, wata mota shakr da rokoki, ta tarwatse, inda ta hadasa mutuwar mutane 11, da su ka hada da sojojin Iraki 3.

A bangaren rundunar Britania, an an yi assarar rayukan sojoji 2, a sahiyar yau litinin, a Bassorah.

A jimilce, sojojin Britania 94 kenan, su ka sheka lahira, a cikin hare hare daban daban, a Iraki, daga mamaye kasar, ya zuwa yanzu.

Baki daya, Engla ta aika sojoji 8.500, a Bassorah, domin kai dauki ga Amurika.

Wannan kashe kashe babu kakkabtawa, sun sa a halin dake ciki, jiragen samma, masu durra angullu,na rundunar Amureuika, sun shiga shawagi a sarrarin samaniyar Bagadaza da sauran manyan biranen kasar Iraki, a yunkurin sojojin amurika, na yakar hare haren ta´addanci.

A cen kuma arewancin kasar, a na ci gaba, da bata kashi tsakanin dakarun Amurika, da yan yakin sunkuru.

A kalla, yan tayawye 13 su ka rasa rayuka, daga yamacin jiya zuwa yau, a cikin barin wuta.7 daga cikin su sun rasa rayuka, a yayin da barin wutar, jiragen samar Amurika ya rutsa da su a massalacin birni Tall Afar.

Gwamnatin kasar Iraki, ta bayana daukar wasu sabin matakai na yaki da hare haren taadanci, daga jerin wannan matakai, gobe idan Allah ya kai mu, za a fara tace zirga zirgar motoci.

A yayin da rikita- rikita ,ke ci gaba da kamari a Iraki, akwai allamun, haske, a yunkurin shinfida zaman lahia tsakanin Isra´ila da hukumar Palestinawa.

Tawagogin kasashen 2, sun kussa cimma daidaito, a kan batu mai sarkakiya, da ya shafi iyakar zirin Gaza, da Misra, bayan majalisar dokokin Isra´ila, ta amince, da kasancewar jamai´an tsaron Misra a karbun iyakar Misra da zirin Gaza.

Shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas, ya gana da wakilin kasar Amurika, dake jagorantar tantanawar da Isr´iala.

Haka zalika, a yunkurin da shuwagabanin kasashen yankin, ke yi, na shawo kan wannan matsala, nan da wani lokaci da ba´a kayyade ba, shugaban kasar Misra, Hosni Mubarak, zai saduwa da praministan Isra´ila Ariel Sharon.

Sannan, Sarki Abdallah, na Jordan, shima, ya bayana kai ziyara ranar alhamis mai zuwa, a Rammallah, inda zai gana, da Mahamud Abbas, a kan matsalar , a na sa ran kuma, zai yada zango a kasar Isra´ila.

A sahiyar yau kuma, tawagar jami´an tsaron Isra´ila da ta Palestinu, sun ziyarci zirin Gaza, domin gane wa idon su, yadda yankin ke ciki, bayan futar Yahudawa yan kaka gida.

A na sa ran ,sati mai zuwa kaddamar da bikin bada zirin na Gaza,a hukunce ga hukumomin Palestinu.