Halin da a ke ciki a Somalia | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da a ke ciki a Somalia

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta bayana aniyar , tura tawaga ta mussamman, ga dakarun musulunci , na ƙasar Somalia wanda a halin yanzu ke rike da Mogadiscio, babban birnin ƙasar, da ma sauran wasu manyan birane.

Kakakin Majalisar Ɗinkin ɗunia mai kulla da ƙasar Somalia Fransois Lonseny Fall, ya sanar manema labarai cewa, a wannan makon ne, ake sa ran aika tawagar, a birnin Jowhar, domin tanana yiwuwar aika agaji zuwa ga al´umomin ƙasar.

Ƙungiyar taraya Afrika, ta buƙaci Majalisar, ta aika dakarun shiga tsakani a Somalia, matakin da

dakarun musulunci ke adawa da shi.

Saidai duk da wannan adawa, shugaban mulkin riƙwan ƙwaryar Somalia, Yusuf Abdullahi, ya gana yau,da sakataran zartaswa na ƙungiyar taraya Afrika, Alfa Umar Konare, a birnin Addis Ababa.

Shugaba Abdoullahi, wanda ke matsayin hoto a kasar Somalia, yayi anfani da wannan dama,domin jaddada buƙatar gwamnatin sa,a game da batun aika tawagar shiga tsakani a Somalia.