Hali rayuwa a Dafur ya tabarbare | Labarai | DW | 07.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hali rayuwa a Dafur ya tabarbare

Shugaban tawagar majalisar ɗinkin duniya a shirin samar da zaman lafiya a Dafur Jan Pronk ya ce halin da ake ciki a Dafur ya yi matukar taázzara duk kuwa da cimma yarjejeniyar sulhu na baya bayan nan. Jakadan na majalisar ɗinkin duniya ya buƙaci dukkan ɓangarorin su martaba yarjejeniyar da aka cimma a watan Mayu a birnin tarayyar Nigeria Abuja domin ɗorewar zaman lafiya a yankin. A wani jawabi da ya yiwa manema labarai a birnin washington shugaban Amurka George W Bush ya gargaɗi Khartoum da cewa gamaiyar ƙasa da ƙasa ba zasu sa ido su bari ana cigaba da tashe tashen hankula a lardin na Dafur ba. ƙoƙarin samun shirin zaman lafiyar na Dafur wanda ƙungiyar gamaiyar Afrika ke shiga tsakani ya sami amincewar gwamnati da ƙungiya ɗaya ne kawai na yan tawayen yayin da sauran ƙungiyoyin yan tawayen suka ki sanya hannu a kan yarjejeniyar. Dubban jamaá sun rasa rayukan su a rikicin na Dafur wanda ya shafe tsawon lokaci fiye da shekaru uku tare kuma da tagaiyar rayuwar mutane kimanin miliyan biyu da rabi.