Halaka Zabiya a Tanzaniya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Halaka Zabiya a Tanzaniya

Ana halaka Zabiya a Tanzaniya saboda camfin cewar gaɓoɓinsu na maganin kuɗi

default

Zabiya na fuskantar barazana game da makomar rayuwarsu a Tanzaniya

A wannan makon mai ƙarewa jaridun na Jamus kusan sun kutsa zuwa kowace kusurwa ta Afirka domin tsegunta wa masu karato ire-iren wainar da ake toyawa a nahiyar a fannoni na siyasa, tattalin arziki da zamantakewa. Amma zamu fara ne da rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung, wadda wakilanta suka leƙa Tanzaniya suka kuma gano wani mummunan abin baƙin ciki a game da farautar Zabiya da ake yi bisa iƙirarin cewar gaɓoɓinsu na maganin kuɗi. Jaridar ta ce:

"A duk faɗin duniya an ƙiyasce yawan Zambiya zai kai dubu ashirin kuma ƙasar Tanzaniya na da Zabiya dubu uku. Amma fa abin takaici shi ne wasu matsafa a ƙasar na iƙirarin cewar gaɓoɓinsu na maganin kuɗi da sarauta da kyautata ɗaɗin rayuwa. Hakan ya sanya wasu miyagun mutane suka shiga farautarsu da yi musu yankar rago a fafutukar neman gaɓoɓin nasu da zasu iya sayarwa ga mabuƙata akan kuɗin da ya kama tsakanin dalar Amirka 2400 zuwa dubu 9600. Kuma ko da yake gwamnati ta ankara da wannan matsala amma ba wani abin da take taɓukawa don ceton rayukan waɗannan bayin Allah."

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel lura tayi da yadda ƙasashen yammaci masu ba da lamuni ke ƙoƙarin taimaka wa Zimbabwe ba tare da an yi ƙorafin cewar suna ƙarfafa wa shugaba Mugabe guiwa ba ne. Jaridar ta ce:

Simbabwe: Robert Mugabe und Morgan Tsvangirai

Shugaba Mugabe da Piraminista Tsivangirai a Zimbabwe

"Zimbabwe na buƙatar taimakon dala miliyan dubu takwas don ta da komaɗar tattalin arziƙinta, kuma tuni bankin duniya da ƙasashen yammaci masu ba da lamuni suka zuba abin da ya kai dala miliyan 630 a ƙasar. Kuma ko da yake da so samu ne da zasu ƙaunaci zuba abin da ya fi hakan, amma tilas su riƙa sara suna duban bakin gatari, ganin cewar har yau ba a shawo kan rikicin da aka yi watanni takwas ana fama da shi tsakanin jam'iyyun gwamnatin haɗin guiwa ta ƙasar ba. Dalili kuwa shi ne kasancewar shugaba Mugabe ne ya fi cin gajiyar wannan haɗin guiwa a sakamakon haka ƙasashen na yammaci ke ƙyamar taimakawa wajen daidaita kasafin kuɗin ƙasar ta kudancin Afirka."

A ƙarƙashin wani sabon shirin zaman lafiyar yankin Darfur da ƙasashen Afirka suka gabatar ana fatan kafa wata kotu ta shiyya wadda zata ci shari'ar miyagun laifuka na yaƙin Darfur, kamar yadda jaridar Berliner Zeitung ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

Rebellen aus der Krisenregion Darfur nehmen Friedensgespräche auf

Ƙungiyar AU na ƙoƙarin ɗinke ɓarakar lardin Darfur

"A ƙarƙashin wannan shiri kotun da za a kafa zata ƙunshi alƙalai daga Sudan da kuma na ƙasa da ƙasa, waɗanda za a ɗora musu alhakin binciken miyagun laifuka na yaƙi da kuma nemo hanyoyin da zasu taimaka a ɗinke ɓarakar dake akwai tsakanin mazauna yankin Darfur."

Allah Ya fuwace wa ƙasashen Afirka ɗimbim albarkatun ƙasa amma duk da haka al'umar nahiyar na fama da ƙuncin rayuwa in ji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce:

Tschad Ölförderung Arbeiter Doba Ölfelder

Ƙasashen Afirka ke da kashi goma cikin ɗari na adanin mai a duniya

"A halin yanzu haka ƙasashen Turai da na Asiya da Amirka ne ke tserereniya a ƙoƙarin cin gajiyar arzƙin da Allah Ya fuwace wa Afirka, wadda ke da kashi 10 cikin ɗari na adanin mai a duniya da kashi 9 cikin ɗari na gas da sauran albarkatu masu ɗimbim yawa da basu lissaftuwa, amma su kansu al'umar nahiyar na fama da bala'in talauci. Murna zata iya komawa ciki muddin ba a nemi wata hanyar da zata taimaka wa makomar rayuwar jama'a a Afirka ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu