Haka ta cimma ruwa a taron kasashen G20 | Siyasa | DW | 12.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Haka ta cimma ruwa a taron kasashen G20

Kasashe ashirin na G20 sun daidaita kan batun tattalin arziki da al'amuran kudi a taron su na Seoul

default

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a taron G20

Shugabannin kasashen G20 masu karfin tattalin arzikin sun kammala taron da suka gudanar a birnin Seuol na Kasar koriya ta kudu tare da nasara kauda sabanin da ake samu tsakanin kasashen wajan rage darajar kudadensu domin samun kasuwa

Abdurahamane Hassane ya yi mana nazari akan muhiman kaidojin da taron ya amince da su.

Kusan dai za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulo domin kuwa duk da irin tankiyar da aka yi ta samu tsakanin shugabannin kasashen wajan amincewa da dokokin a karshe dai an samu fahimtar juna akan batutuwan da suka hadda da cimma yarjejeniyar fito dakuma wasu sauran matakai na magance rashin daidaito ta fuskar kasuwancin duniya wanda daman shine babban abinda ke kawo cikas ga ci- gaban kasasahen.

Haka kuma taron ya amince da sake fasalin asusun bayar da lamuni na duniya wato IMF ta yadda wasu kasasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa zasu sami karfin fada a ji.

Wani babban gurin da shugabannin kasashen suka sama gaba shine na kafa wani sabon tsari da zai bayar da damar gwada mizanin koma bayan tattalin arziki duniya domin kaucewa ga jeffa tattalin arzikin duniya cikin wani mawuyacin hali

Ko da shike wasu manazarta na ganin manufofin da taron ya cimma su kasance marasa tabas to amma kwararu na ganin wadanan matakai zasu kasance wani riga kafi ga tattalin arziki na duniya. Angela Merkel shugabar gwamnatin jamus ta yi korafin cewa an cimma nasara.

"Mun yi nazari so sai ina tsamani a jumulce sanarwa karshen ta kumshi du abinda ya kamata kuma ina tsamanin Amurka za ta bada gudu mowarta na tabatar da tsare tsare da aka cimma"

A yanzu wannan nauyi na wannan aiki an ratayasa akan wuyan ministocin kudi na kungiyar tare da hadin gwiwar hukumar ta tsara kudade na duniya domin pulo da tsarin da ya dace kafin nan da watanni shidda na farkon sabuwar shekara ta 201.1

Sanarwar karshe ta yi kira ga wasu kasashen na kungiyar da su daina rage darajar kudadensu da nufin samun kasuwa ga kayan da suke kirkiro.

Kasashen China da Amurka dai sune ke zargin junansu kan wannan batu wanda kuma ake da jikara ka ya ci gaba da zama kalubale, to amma shugaban Amurka Barack Obama ya shaida cewa babu wani tababa.

"Ya ce na san cece ku ce zai ci gaba da yaduwa ne akan sabanin da ake samu amma ina gani a wannan taro da muka gudanar mun dinke barakar da ke da a kwai kuma yanzu muna kan hanyar nasara."

Mayan kungiyoyi na duniya irin su oxfam da save the children sun yi marhabin da yunkurin na kasahen akan bukatar bayar da taimako ga kasashe masu tasowa dake fama da talauci dakuma Yuan.

kyauwan alkawari dai shine cikawa wannan kuma itace ayar tambaya da sauran kasashe na duniya suke azawa kansu dangane da wadanan sauye sauye da aka samu daga shubannin kasashe masu arziki massana antu.

Shgaban kasar Rasha Dimitri Medvedve ya yi gargadin cewa tilas sai an zage damtse kafin samun biyan bukata.

"Matakan da aka dauka a wannan ganawa ba zasu tabata sai da bada hima dakuma hadin kai na sauran kasashen domin a kaucewa irin tarnakin da akan samu a kan shanin musaynar kudi."