1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hadin kai da kasashen Africa

Ganawar shugaban kasa na Jamus, Horst Köhler da shugabannin Afrika domin karfafa hadin kai tsakanin su

Shugaban kasar Jamus, Horst Köhler

Shugaban kasar Jamus, Horst Köhler

Afrika nahiya ce dake fama da matsaloli masu tarin yawa. Daga cikin su, akwai rikice-rikice, yake yake da bala’oi iri dabam dabam. Babu wasu rahotanni dake fitowa daga wnanan nahiya a kullum rana ta Allah, in banda wadanda suka shafi yunwa, fama da cutar AIDS, ko matsalar cin rashawa. To amma abin tambaya shine: menene ainihin tushen wadannan matsaloli da suka addabi nahiyar Afrika? Shin wane irin nauyi ne da ya rataya a wuyan manyan kasashen duniya masu arziki game da nahiyar Afrika. Shin kasashen arewa, masu ci gaban masana’antu da kasashe na kudu, masu tasowa, kawayen juna ne, kuma masu hadin kai da juna? Me ya sanya duk wani shiri na taimakon raya kasa baya samun nasara a wnanan nahiya ta Afrika. Wadannan dai suna daga cikin tambayoyin da za’a yi kokarin amsa su, lokacin wani taro da shugaban kasa na Jamus ya kira a nan Bonn tun daga gobe, inda aka gaiyaci wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika, domin nazari tare dasu.

Taron da shugaban na Jamus, Horst Köhler yayi gaiyatar sa a gobe, za’a yi shi ne karkashin taken: hadin kai da kasashen Afrika. Wannan taro burin sa shine ya shigar da sabon jini da sabon tunani a cikin dangantakar dake tsakanin kasashen Afrika da kasashe masu ci gaban masana’antu da kuma nazarin matsaloli da wahalolin da nahiyar ta Afrika take fama dasu, ba tare da wata rufa-rufa ba, tsakanin bangarorin biyu gaba da gaba. Irin wnanan kudiri dai yana daga ckin manyan al’amuran da shugaban kasa, Horst Köhler ya lashi takobin aiwatar dasu a tsawon shekaru biyar da zai yi kann wnanan mukami. Tun daga gobe Asabar da kuma jibi Lahadi, manyan bakin da shugaban ya gaiyata zasu tattauna game da matsayin dangantaka tsakanin kasashen masu tasowa da masu ci gaban masana’antu a Bonn.

Taron dai shine mafi girma da wani shugaban kasa na Jamus ya taba shiryawa, domin duba nahiyar Afrika. Tattaunawar da za’a yi a fadar shugaban kasa ta Villa Hammerschmidt da masaukin manyan baki na gwamnatin taraiya a Petersberg duka a Bonn, zata hade shugabannin kasashen Afrika biyar ne da tsoffin shugabanni biyu. Cikin mahalarta taron har da Thabo Mbeki da Afrika ta kudu da Olusegun Obasanjo na Nijeriya da Joaquim Chissano na Mozambique, sai shugaba Alpha Oumar Konare na Mali, a matsayin sa na shugaban hukumar kungiyar hadin kann Afrika. Kazalika, an gaiyaci marubucin adabi na Nijeriya, Wole Soyinka, da ya taba samun lambar adabi ta Nobel, sai kuma marubucin nan dan kasar Sweden, Henning Mankell dake zaune a Mozambique, tare da manyan masu masana’antu da yan kasuwa da masu ilimi da yan jarida daga nahiyar Turai da Afrika.

Tare dasu gaba daya, shugaban na Jamus zai yi kokarin binciko yadda za’a iya samun hadin kai na hakika, tsakanin kasashen Afrika da kasashe masu ci gaban masana’antu da kuma gano abubnuwan dake hana samun irin wanan hadin kai a matsayi na daidai wa daida tsakanin bangarorin biyu. Tun a jawabin sa na farko, lokacin da aka zabe shi kann mkukamin shugaban kasa, Hoerst Köhler yace shi a gareshi, makomar nahiyar Afrika zata zama yar manuniya kann yadda duniya ta dauki abin da ake kira hadin kai.

A zamanin da yake rike da mukamin darektan hukumar kudi ta duniya, Horst Köhler ya ziyarci wnanan nahiya akalla sau shidda. Ya sadu da mafi yawan shugabanni da masu fadi aji a wannan yanki, kuma ko da ya zama shugaban kasa a Jamus, ya ci gaba da nuna cewar da gaske yake yi a game da kyautata makomar nahiyar ta Afrika. Ziyarar sa ta farko a bara, zuwa wajen nahiyar Turai a matsayin shugaban kasa, ta kai shi ne zuwa kasashen Saliyo, Benin, Habasha da Djubuti. Yace a duk tsawon zamanin sa na mulki, zai ci gaba da tuntubar nahiyar Afrika. Wannan taro da ya gaiyata na hadin kai da Afrika, wata manufa ce dangane da cimma wnanan buri. Shugaban na Jamus ya kara da cewar:

A Afrika, ana fama da matsaloli da mummunan hali na kaka-ni-kayi. To amma wnanan ba shine gaskiyar al’amarin gaba daya ba. Duk da wnanan mummunan yanayi da halin kaka-ni-kayi, na lura da cewar al’ummar nahiyar Afrika suna jin dadin rayuwar su, suna da karfin zuciya da alfahari da kansu, wadanda a nan Turai ana ganin su a matsayin ba a bakin komai suke ba. Na ga aiyukan raya kasa masu tarin yawa wadanda suka tabbatar da kwazo da karfin zuiciyar nahiyar Afrika, wadanda ba duka ko ina akr samun kamar su ba.

Shugaban na Jamus yace yana fatan ganin nahiyar Turai da zata tabbatar da aiwatar da aiyukan taimakon rasa da zasu cimma burin majalisar dinkin dunmiya, ba kawai ta fatar baka ba, amma a zahiri: wato a takaice, wadannan kasashe na TUrai su kara bude kasuwanin su ga kayaiyaki daga kasashe matalauta, tareda kara yawan kudade da gwamnatoci suke warewa a matsayin taimakon raya kasa.