HADARIN SPAIN | Siyasa | DW | 12.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HADARIN SPAIN

Jamiin na MDD yayi wannan furucin ne a taron da majalisar dunkin duniya ta gudanar da wasu kasashe 55 dangane da harkokin tsaro da yaki da taaddanci na yini biyu da aka kammala yau.Taron yayi nuni dacewa mafi yawan kasashe na nuna halin ko oho wajen daukan matakai na kare rayukan jamaarsu daga tsageru da suka shahara wajen kashe kashe.Taron ya cimma fitar da sanarwar bayan taro dake bukatar kasashen duniya su mike tsaye wajen yakan yan taadda. Sanarwar bugu da kari tayi kira ga kasashen dake maida hankali kann wasu batutuwa ,dasu sanya fifiko wajen kalubalantar wannan matsala data zama ruwan dare gama duniya.Duk da cewa babu tabbaci kann kungiyar dake alhakin kai wannan hari,ana zargin kungiyar tsageru ta Basque din ETA da harin.Bayan gwajin boma boman da akayi amfasni dasu a harin na jiya,maaikatar harkokin cikin gida na Spain ta sanar dacewa suna da alaka da wadanda yan kungiyar ETA ke amfani dasu wajen kai hare hare.

A halin yanzu dai alkaluma na nuni dac ewa mutane 199 suka rasa rayukansu a harin na birnin madrid na jiya da safe,ayayinda kimanin 1,400 suka samu raunuka,daga cikinsu kuwa 377 na cikin hali mawuyaci na jinya a asibitocin kasar.

Ayayinda kasashen duniya ke cigaba da aikewa da sakonni taaziyya wa gwamnatin Spain dangane da wannan asara da tayi,fadar gwamnatin Amurka ta amince da bawa Spain tallafi dangane da binciken wadanda keda alhakin kai wadannan hare hare wa jiragen pasinja guda 4 a jiya. Acan birnin Madrid kuwa jamiai sun duka kain da nain wajen binciken wadanda keda hannu a wannan harin.Acan kasar Itali kuwa ministan harkokin kasar ya bada umurnin sake nazarin dokokin yaki da ayyukan yan taadda a wannan kasa.Bayan harin kunar bakin waken daya ritsa da Amurka a shekara ta 2001,kasashe da dama sun dauki matakai tsaurara dangane ayyukan tarzoma da taaddanci.

Shi kuwa Prime ministan Ireland Bertie Ahern dake rike da kewayen shugaban kungiyar tarayyar Turai Eu,yayi kira ga jammaa dake kasashe 15 dake wannan kungiya dasuyi wadanda suka rasa rayukansu addua na musamman ranar litinin.Ayayinda kasar Girka ta nemi taimakon kungiyar tsaro ta NATO ,wajen tabbatar da tsaro lokacin gasar wasannin motsa jiki na Olympics.A nashi bangare shugaba Jacques Chirac na faransa ya gana da manyan masu bashi shawarwari dangane matakan tsaro bayan harin na Madrid a jiya.Anan Jamus kuwa alummar jihohin Bavaria da Duesseldof sun sanar da daukan matakan tsaro a tashoshin jirgin kasa.shugaban gwamnati Gehard Schroder yace jammian tsaro na tabbatar dacewa,barazanar tsaro bata karu ba a cikin kasar.
 • Kwanan wata 12.03.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlL
 • Kwanan wata 12.03.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlL