Hadarin jirgin saman fasinja a Nijeriya | Labarai | DW | 10.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin saman fasinja a Nijeriya

Kusan dukkan mutanen da ke cikin wani jirgin saman fasinja da yayi hadari a birnin Fatakwal dake kudancin tarayyar Nijeriya sun rasu. Tashar radiyo ta Rhythm FM wadda ta fara ba da labarin aukuwar hadarin ta ce jirgin saman mallakin kamfanin Sosoliso dauke da fasinjo sama da 110 ya taso ne daga birnin Abuja amma ya fadi kuma ya kama da wuta lokacin da ya zo sauka a filin jirgin saman birnin na Fatakwal. Wani jami´in hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama a Nijeriya ya ce an gano gawawwaki 60 sannan mutane 7 sun tsallake rijiya da baya a wannan hadarin. Jami´in ya ce yanzu haka ana nan ana gudanar da aikin ceto. Rahotannin da ke iso mana daga birnin na Fatakwal na cewa akwai dalibai 75 na wata makarantar sakadandare a cikin jirgin jirgin. Wannan hadarin dai ya auku ne kasa da wata biyu bayan faduwar wani jirgin saman fasinjan kamfanin Bellview a kusa da birnin Legas wanda ya halaka dukkan mutane sama da 100 dake cikin jirgin.