Hadarin jirgin sama a Senegal | Labarai | DW | 06.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin sama a Senegal

Wani jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hadari a kan hanyarsa ta isa Dakar dauke da mutane bakwai ciki kuwa har da wani mara lafiya dan kasar Faransa.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Sanegal ta sanar da cewa jirgin mallakar wani kamfani mai zaman kansa na kasar ya taso ne daga Ouagadougou na kasar Burkina Faso kuma ya bace an daina jin duriyarsa tun a yammacin wannan Asabar da misalin karfe bakwai agogon GMT a yayin da yake kimanin nisan kilomita 111 da yammacin Dakar babban birnin kasar ta Senegal. Tuni dai dakarun sojojin sama na kasar ta Senegal suka isa inda ake kyautata zaton jirgin ya fadi domin gudanar da bincike.