Hadarin jirgin sama a Indonesiya | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin sama a Indonesiya

Wani jirgin saman fasinja na kasar Indonesia ya kama da wuta yayinda ya sauka a wani filin jirgin sama na birnin Yogyyakarta na kasar ta Indonesia.

Rahotanni sunce akalla mutane 49 suka rasa rayukansu .

Ministan sufuri na Indonesia Hatta Rajasa yace akalla mutane 73 suka tsira da ransu daga wannan hadari.

Jamiian filin jirgin sunce jirgin ya zarce inda ya kamata ya tsaya ne bayan ya sauka.

Pasinjoji fiye da 140 ne suka cikin jirgin a lokacinda ya taso daga birnin Jakarta,cikinsu har da wasu jamian diplomasiya da yan jaridu na kasar Australia.