Hadarin jirgin ƙasa a Congo | Labarai | DW | 03.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin ƙasa a Congo

Kimanin mutane 100 ne suka rasa rayukan su wasu da dama kuma suka jikata bayan da wani jirgin ƙasa ya goce daga kan hanyar sa a wani ƙauye a jamhuriyar dimokraɗiyar Congo. Haɗarin ya auku ne a wani yanki mai tazarar kilomita 200 daga arewa maso yammacin Kananga babban birnin gundumar kasai.Ministan yaɗa labarai na ƙasar Toussaint Tshilombo yace an kafa kwamiti domin binciken musabbabin haɗarin. Shugaban ƙasar Joseph Kabila da P/M Antoine Gizenga sun tura tawaga ta musamman domin nazarin haɗarin tare da taimakawa mutanen da lamarin ya shafa. Ana dai samun yawaitar haɗuran jiragen ƙasa a Jamhuriyar ta Congo sakamakon rashin kula da gyaran hanyar dogon tun bayan samun mulkin kan ƙasar a shekarar 1960.