Hadarin jirgi a Nigeria ya kashe Sultan Sokoto | Labarai | DW | 29.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgi a Nigeria ya kashe Sultan Sokoto

Mutane shida ne suka tsira da rayukansu daga hatsarin jirgin sama na Pasinja daya auku yau a abuja,fadar gwamnatin tarayyar Nigeria,sakamakon iskar guguwa jim kadan da tashinsa daga filin saukan jiragen sama na Dr Nnamdi Azikiwe.Kusan dukkan sauran fasinjoji daga cikin 104 dake wannan jirgi dai sun rasa rayukansu,.Rahotannin kawo yanzu sun tabbatar dacewa daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu a hadarin jirgin saman ,harda sarkin Musulmi Mohammadu Maccido,da wasdu manyan jamian gwamnatin Jihar Sokkoto.Wannan shine karo na uku da aka samu hadarin jirgin sama a tarayyar Nigeria cikin tsukin shekara guda.