1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HADARIN JIRGI A IRAN YA KASHE MUTUM 200

ZAINAB AM ABUBAKARFebruary 18, 2004
https://p.dw.com/p/Bvln

Jirgin wanda ke tafiya a yankin arewa maso gabashin kasar ta Iran,kamar yadda rahotanni suka nunar yana dauke ne da sinadran masanaantu,takin zamani da man petur,inda nan take ya kama da wuta wanda yayi sanadiyyar kashe mutane tsakanin 60 zuwa 200,kana daruruwa suka samu rauni,ayayinda kauyuka 5 dake yankin sun lalace.

Hadarin dai ya auku ne a birnin Neyshabur,mai tazarar km 650 gabashin fadar kasar dake tehran.Akalla akwai jerin motoci 51 dake tsaye a tashar jirgin kasa na Abu Muslim a wannan gari.An dai kiyaszta cewa kimanin mutane 200 suka rasa rayukansu ayayinda 300 suka samu raunuka na kuna,akasarin wadanda suka rasa rayukan nasu jamian agaji ne ,ayayinda motocin dake jira akwashe su suka dinga bindiga sakamakon wannan gobara.To sai dai rahotanin kafofin yada labaru na yankin sun sanar dacewa akasarin kauyukan biyar dake wannan hanya sun kama da wuta,ayayinda mutane akalla 60 suka rigamu gidan gaskiya.

Bugu da karti gidan talabijin din wannan kasa ta nuna hotunan yadda tarogon jirgin ke cigaba da cin wuta,ayayinda gidaje ahannu guda suzka kone kurmus.Jamiai ya zuwa yanzu sun bayyana cewa ana iya fuskantar bindigan sauran taragogi dake dauke da sinadran na masanaanta,sai dai asna iyakan kokarin ganin cewa hadarin bai kara muni ba.Mataimakin gwamna general na gunduwar Khorassan,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP ta wayan tangaraho cewa ,akwai jamiaan gwamnati biyu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu.wadanda suka hada da gwamnan birnin Neyshabour Mojtaba Farahmand,da babban jamiin kula da tashar samar da wutan lantarki Morteza Fahrian,da magajin garin. Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun dada tabbatar dacewa akalla mutane 200 sun rigamu gidan gaskiya,ayayinda kimanin 350 suka samu raunuka Idan baa manta ba a ranar 26 ga watan Disamban shekarar data gabata ne akayi girgizar kasa a Iran wanda ya kashe samada mutane dubu 40 a garin Bam dake yankin kudu maso gabashin wannan kasa.