Hada-hadar diplomatia domin warware yaƙin Isra´ila da Hezbollah
July 27, 2006Talla
A fagen diplomatia kuwa, ƙasar France, ta gabatar da wani pasali ga komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, wanda a ganin shugaba Jaques Chirak, zai samar da masalahar tsakanin ɓangarorin 2.
Shawarwarin na France sun hada da girka wani yankinna mussamman, tsakanin kudancin Labanon da Isra´ila, bisa kular Majalisar Ɗinkin Dunia.
Kamin samo bakin zaren warware wannan rikici, a halin yanzu dakarun Isra´ila da na Hezbollah na ci gaba da masanyar wuta, inda a ƙalla mutane 10 su ka rasa rayuka a gumurzun da aka yi yau.