1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha zata janye dakarunta daga kan iyakar ta da Eritrea

December 10, 2005
https://p.dw.com/p/BvH9

Kasar Habasha ta ce a shirye ta ke ta janye dakarunta daga kan iyakar ta da Eritrea da suke takaddama akai. Habasha ta ce zata yi haka ne don nuna biyayya ga wani kudurin kwamitin sulhun MDD wanda yayi barazanar sanya takunkumi. Kamfanin dillancin Labarun kasar ENA ya rawaito ministan harkokin waje Seyoum Mesfin na cewa don samar da wanzuwar zaman lafiya a shirye Habasha ta ke ta janye dakarunta don hakan ta dace da kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1640. Ganin yadda Habasha da Eritrea ke kara girke dakaru akan iyakar su, musamman bayan mummunar yakin kan iyaka da suka gwabza daga shekarar 1998 zuwa ta 2000, a cikin watan da ya gabata kwamitin sulhu yayi barazanar kakabawa kasashen biyu makwabtan juna takunkumin karya tattalin arziki da na diplomasiya idan suka sake ba hamata iska.