Habasha: Zanga-zanga kan mutuwar mutane
October 3, 2016Talla
Shaidun gani da ido suka ce mutane ne da dama suka fantsama kan titunan Ambo da Bule Hora da sauran garuruwa da ke Oromiya don nuna fushinsu biyo bayan rashin da aka yi a jiya Lahadi. Wani dalibin jami'a da ya zabi a sakaya sunansa ya ce ya ji harbe-harbe lokacin da ake zanga-zangar kafin daga bisani komai ya lafa, inda ya kara da cewar daga baya titunan a Ambo sun kasance ba kowa a kansu kana sanan lamura sun tsaya cik. A wasu yankunan kuma mazauna wuraren sun bada labarin arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro sai dai ya zuwa babu labari da aka samu na asarar rai.