1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Abiy zai zama sabon Firaminista

Abdullahi Tanko Bala
March 28, 2018

Kawancen Jamiyyu da ke mulki a kasar Habasha EPRDF sun nada Dr Abiy Ali a matsayin jagora wanda kuma shine zai zama sabon Firaministan kasar.

https://p.dw.com/p/2v9lZ
Äthiopien Abiy Ahmed OPDO
Hoto: Abdulbasit Abdulsemed

Wannan shine karon farko a tarihi da wani dan kabilar Oromo, kabila mafi girma a kasar Habasha zai rike mukamin Firaminista inda zai maye gurbin tsohon Firaminista Hailemariam Desalegn wanda ya yi murabus. Shin wanene Dr Abiy Ali? 

An haife shi a shekarar 1976 a yankin Jimma dake yammacin Habasha. Sabon shugaban Dr Abiy Ahmed Ali dan shekaru 41 da haihuwa, Allah ya yi masa baiwa ta fasahar iya magana yana kuma jin wasu harsuna da dama. Nadin sabon shugaban ya kasance matakin kawo karshen tsawon makonni da aka kwashe ana muhawara kan samo bakin zaren dinke barakar da aka samu a kasar.

Abiye Ahmed in Addis Ababa
Dr Abiye Ahmed sabon jagoran kasar HabashaHoto: Reuters/Stinger

Tun yana karami Abiy ya shiga gwagwarmayar siyasa a kasar inda ya bi sahun kungiyar adawa da gwamnatin Mengistu Hailemariam. Ya shiga aikin rundunar sojin Habasha inda ya sami gogewa a fannin tattara da bayan sirri ya kuma kai har mukamin Laftanan Kanar.

Sakamakon kisan kiyashi a Rwanda a 1993, Abiy ya yi aiki a rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya UNAMIR domin tabbatar da tsaro da kare lafiya sannan daga bisani aka tura shi aikin tsaro a kan iyakar Habaka da Eritrea.

Äthiopien vor der Wahl EPRDF Anhänger in Addis Abeba
Wani matashi dauke da tutar EPRDF mai mulki Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Sai dai kuma a cewar matasan yankin Oromo ba za su yarda da batun wai naka, naka ne ba, abin da suke bukata shine su ga sauyi , kamar yadda wani dan kabilar ya shaidawa DW. 

A waje guda masu sharhi kan al'amuran yau da kullum kamar Mengistu Assefa ya baiyana shakku akan ko Abiy zai iya kawo wani sauyi. 

A nasu bangaren kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Habasha da sauran yankuna  sun yi kiran gudanar taron kasa da zummar tattaunawa domin sasanta al'umma da hadin kan kasa. Sabon shugaban na Habasha Abiy Ali yana mace daya da kuma yaya mata uku. Ya yi digiri na biyu a fannin daidaita ci gaba da kuma digirin digirgir a fannin sulhunta rigingimu