Haɗin kan Pakistan ga yaƙi da tarzoma. | Labarai | DW | 16.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗin kan Pakistan ga yaƙi da tarzoma.

Hukumomin Pakistan sun ce mai yiwuwa ne su miƙawa Britaniya Rashid Rauf babban mutumin da ake zargi da shirya maƙarƙashiyar harin bom ɗin jiragen saman da bai yi nasara ba. Kakakin maáikatar harkokin wajen Pakistan Tasnim Aslam tace ko da yake har yanzu basu sami buƙatar hakan daga mahukuntan Britaniya ba, to amma ta ce Pakistan na iya tasa ƙeyar sa zuwa London. Ta ce za su cigaba da sa ido tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa. Rashid Rauf wanda ɗan ƙasar Britaniya ne ana zargin cewa ɗan ƙungiyar al-Qaída ne, kuma ya bada bayani dalla dalla a game da harin bayan da aka kama shi a farkon wannan watan. Mahukuntan Britaniya sun kama mutane da dama waɗanda ake zargi da hannu a shirin harin taáddancin.