Haɗin gwiwar Jamus da Amurka kan Ta′addanci | Siyasa | DW | 11.03.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Haɗin gwiwar Jamus da Amurka kan Ta'addanci

Amurka da Jamus sun kulla dangantakar yaki da ta'addanci

default

Ministan cikin gida na Jamus, Wolfgang Schaeuble


Ƙasashen Amurka da Jamus na fatan kara kyautata hadin kai da musayar rahotanni tsakaninsu a matakai na ƙasa da ƙasa domin yaki da ta'addanci da kuma miyagun laifuka. Ministocin cikin gida da na shari'a na kasashen biyu sun cimma daidaituwa akan wata takarda ta yarjejeniya akan wannan manufa.
Ƙasashen na Amurka da Jamus na fatan yin koyi ne da wata yarjejeniyar da wasu kasashen Turai su bakwai suka cimma a shekara ta 2005 akan musayar bayanai tsakaninsu a fafutukar murkushe ayyukan ta'addanci da miyagun laifuka. To sai dai kuma ta la'akari da wasu ayyuka da hukumar leken asrin Amurka ta CIA ta sha aikatawa a harabar kasashen Turai ba a bisa ka'ida ba, ministan harkokin cikin gidan Jamus Wolfgang Schäuble yayi nuni da cewar yarjejeniyar tsakanin Jamus da Amurka ta kunshi manufofin kare bayanai na jama'a dake tattare a cikin yarjejeniyar kasashen Turai. Schäuble ya ci gaba da cewar: "Ina so in kara tunasarwa ne cewar a karkashin yarjejeniyar kasashen Turai da aka fi sani da yarjejeniyar Prüm sai da aka ya ba wa tsari da kuma ka'idojin da aka shimfida na kare bayanan da ake tarawa game da mutane a wawware, wanda zai iya zama abin koyi ga sauran yarjeniyoyin da za a cimma akan irin wannan manufa nan gaba." Ita ma ministar shari'a ta Jamus Brigitte Zypries sai da ta jaddada hakan ta kuma yi nuni da kariya ta doka da aka shigar a yarjejeniyar. Ta haka nan gaba, misali, Amurka zata zama ita ce kawai ke da ikon ba da izinin tara bayanai akan wani mutumin da ake nema ruwa a jallo da ake da hoton hoton tambarin babbar yatsarsa. Dangane da bayanai da suka shafi yanayin halitta, kamar gwajin nan na DNA babu wata daidaituwar da aka cimma kawo yanzu saboda hatta a Amurka babu wata dokar dake zama gishikin musayar wadannan bayanai, in ji sakataren cikin gida na kasar Micheal Chertoff. Bugu da kari kuma kasashen Turai sun fi Amurka ci gaba a wannan fanni. Chertoff yayi madalla da yarjejeniyar da aka cimma inda yake cewar fafutuka ake domin murkushe abokan gaba dake gudanar da ayyukansu tsakanin kasa da kasa saboda haka ya zama wajibi a tinkare su a dukkan sassa na duniya. Yarjejeniya na ba da damar fadakar da abokan hulda a game da duk wani mutumin da ake tababa game da kasancewarsa dan ta'adda ko mai aikata miyagun laifuka. Ga sakataren cikin gida na Amurka, wannan maganar tana da muhimmanci, inda yake cewar: "Wannan kudurin zai ba mu ikon farautar 'yan ta'adda da masu aikata miyagun laifuka a ketaren iyakokin kasashe tare da cafkesu da karya alkadarinsu kafin su wanzar da danyyen aikinsu. A lokaci guda kuma yarjejeniyar tana ba da cikakkiyar kariya ga bayanai da aka tara game da mutanen da ba ruwansu, wanda shi ne ainihin ginshikin zama na demokradiyya." To sai dai kuma Peter Schaar, wakilin gwamnatin Jamus akan matakan kare bayanai na al'uma, ya bayyana tababarsa game da wannan furuci. Domin kuwa, kamar yadda ya ce dokokin kare bayanai na al'uma a Amurka ba su aiki a kasashen ketare. Shi ma kakakin 'yan hamayya akan al'amuran doka Max Stadler, ko da yake yayi madalla da yarjejeniyar, amma sai ya kara da cewar: "Bai kamata a rika musayar bayanai akan daidaikun mutane ko ta halin kaka ba, sai dai kawai wadanda suka shafi mutane da akwai shaida game da su. In kuwa ba haka ba za a yi wani abin da daga bisani zai haifar da da na sani." Ala-kulli halin dai za a tattauna kudurorin yarjejeniyar a majalisar dokoki ta Bundestag kafin a albarkace ta nan gaba.