Haɗarin jirgin sojojin ƙasar Lybia a birnin Kusseri na Cameroun | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin jirgin sojojin ƙasar Lybia a birnin Kusseri na Cameroun

Wani jirgin samar sojojin ƙasar Lybia, ya yi hatsari cikin wata unguwa, ta birnin Kusseri na ƙasar Kamaru , kussa da iyaka tasakanin Tchad da kamaru,a sahiyar yau lahadi.

Rahotani daga inda hatsarin ya wakana, sun nunar da cewa, baki ɗaya, matuka jirgin 6, sun rasa rayuka.

Magajin garin birnin Kusseri , ɗan Majalissa Kamssulum Abba Kebir, ya sannar da kamapanin dullancin labaran France, cewa, haɗarin ya abku, bayan da jirgin ya samu matsaloli, wajen sauka a filin saukar jiragen sama na birnin N´Djamena a ƙasar Tchad.

Wanda su ka ganewa idon su, al´amarin,sun ce baki ɗaya jirgin ya ƙone ƙurmus.

Saidai,banda matuƙan sa, babu wanda su ka rasa rayuka, daga ɓangaren mazauna unguwar da ya faɗi.