Haɗarin jirgin sama a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo | Labarai | DW | 04.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin jirgin sama a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo

A Jamhuriya Demokradiyar Kongo, wani jirgin samar ɗaukar kaya, tare da mutane kimanin 20 a cikin sa ya yi sala da ka, a kussa da birnin Kinshassa.

Sanarwa daga hukumomin ƙasar sun ce jirgin kira Antonov mai lamba 26 mallakar kampani Afrika One, ya bankaɗi wani gida, dake ke unguwar Masina, kusa da filin saukar jiragen samar birnin Kinshassa.

A nan take ya da wuta, ya kuma ƙone ƙurmus.

Jamhuriya Demokradiyar Kongo, na ɗaya daga ƙasashen Afrika, da su ka yi ƙaurin suna ta fannin yawan haɗarurukan jiragesn sama.

Kasar ta mallaki kampanoni zirga-zirgar jirage da dama , to saidai mafi yawan su, nada tsoffafin jirage ƙira ƙasar Russia.

Gwamnati ta bayana buɗa bincike, domin gano mussababbin haɗarin na yau, tare da kuma ɗaukar matakan daidaita harakokin suhurin jiragen sama a ƙasar baki ɗaya.