Haɗarin jirgin ruwa a Bahrain | Labarai | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin jirgin ruwa a Bahrain

A ƙalla mutane 53 ne suka rasa rayukan su a yayin da wani jirgin yan yawon shaƙatawa ya nutse a gaɓar kogin Baharmaliya. An ruwaito cewa jirgin na ɗauke da mutane kimanin 130 waɗanda suka haɗa da Amurkawa da yan Britaniya da Filifins da Afrika ta kudu da Masar da India da kuma yan ƙasar Bangladesh. Rahotanni sun baiyana cewa ya zuwa yanzu maáikatan agaji sun sami ceto a ƙalla mutane 63. Babu rahoton cewa nutsewar jirgin na da nasaba da ayyukan yan taádda.