1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin jirgin Comair a Amurika ya hadasa asara rayuka da dama.

Shugaban kampanin zirga zirgar jiragen sama, Comair, na ƙasar Amurika, ya tabbatar da mutuwar mutane 49, daga jimmillar mutane 50, da wani jirgin sa, ke ɗauke da su, a haɗarin da ya rutsa da shi, jim kaɗan bayan tashin sa, daga filin saukar jiragen sama na Lexingtone dake gabas maso tsakiyar Amurika.

Mutun ɗaya tilo, ya ƙetara rijiya da baya, a cikin wannan haɗari, wanda ya zuwa yanzu, babu cikkakar masaniya a kan abinda ya hadasa shi.

Wannan shine haɗarin jirgi mafi muni, a Amurika tun shekara ta 2001, inda wani jirgi ƙirar Airbus na kampanin American Airlines ya tarwatse a kewayen birnin Newyork, wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar passenjoji 260.

A halin da ake ciki, jami´an tsaro sun fara bincike, domin gano mussabbabin faɗuwar jirgin na Comair.